✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban ga dalilin da Najeriya za ta rika shigo da man fetur daga waje ba – Indimi

A tattaunawa ta musamman da Aminiya ta yi da fitattacen dan kasuwar nan Alhaji Muhammadu Indimi kan rayuwarsa ya ce bai ga dalilin da Najeriya…

A tattaunawa ta musamman da Aminiya ta yi da fitattacen dan kasuwar nan Alhaji Muhammadu Indimi kan rayuwarsa ya ce bai ga dalilin da Najeriya za ta rika shigo da man fetur daga waje ba, bayan ga matatunta na mai. Ya ce idan  mutum guda kamar Dangote zai iya gina matatar man fetur, babu dalilin da gwamnati za ta gaza yin haka:

A ina kake zama idan ka je kasar Amurka?

Duk lokacin da na tafi nakan sauka ko in zauna a Miami, to amma tunda na shiga harkar kasuwancin man fetur nakan sauka ne a Cibiyar Kasuwancin Mai ta Duniya wato Houston don ina da gida da ofishi a can. Kuma ofishina na fasaha da kere-kere a Najeriya yana Legas ne, a yayin da babban ofishina ke Abuja.

To ranka ya dade an san ka da kyautata wa al’umma ta fuskar inganta rayuwarsu, kamar mutane nawa ne za a iya cewa sun ci moriyar kyautatatawar taka?

Yana daya daga cikin ayyukanta, ita Masana’antata wato (Oriental Energy Resources Limited, OERL) ta agaza wa al’umma don inganta rayuwarsu. Na gina rukunin gidaje a Enwang na kimanin Naira miliyan 700, tare da bayar da tallafin  gurbin karatu (scholarship) ga daliban Jihar Akwa Ibom su 470, kaddamar da daukar nauyin wani shiri a wani bangaren karatun harkar sarrafa man fetur a Jami’ar Uyo, baya ga aikin kyautatawa har ila yau mun bayar da gudunmawarmu a Cibiyar Kasuwanci ta Duniya da take Jami’ar Lynn a kasar Amurka. Duk dai burinmu mu ga cewa mun bayar da gudunmawarmu a fannoni da dama irin su kiwon lafiya da ilimi da kuma jin dadin jama’a. Don haka muka kaddamar da Gidauniyar Muhammadu Indimi, (MIF) da nufin daukaka darajar daruruwan al’umma tare da fitar da su daga cikin kangin yunwa, cututtuka, jahilci da fatara a Arewacin Najeriya, a shekarar 2006. Gidauniyar Indimi ta dauki nauyin karatun daruruwan dalibai musanmman wadanda suka fito daga jihohin Borno da Yobe zuwa Jami’ar Africa International da take kasar Sudan. Kuma ta taimaka wa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a yankin Arewa maso Gabas, ta fuskar samar musu da abinci,  tufafi, dakunan shan magani, musamman ga ’yan gudun hijira a Jihar Borno  akasarin sansanonin gudun hijirar da suke.

To yaya habaka da girman masa’antarka take?

Ai na fada maka cewa wannan baiwa ce kawai daga Ubangiji, domin ban taba halartar wata makarantar boko ba, amma ka ga a kowace shekara ina taimaka wa daliban makarantu har zuwa karatunsu na jami’a sama da  dalibai 100. Kudin samar da gurbin karatu, ban taba damuwa ba, maimakon haka ina mai gode wa Allah, domin idan kana da kudi to abin da ka bayar shi ne naka, abin da kuma ka ci to ba naka ba ne domin za ka kasayar da shi. To haka na yi imani da abin dole ne mutum ya taimaka wa al’umma domin taimakon al’umma shi ne zai cece ka ranar gobe Kiyama.

 Kana da shekara nawa ka  yi aure?

Ina da shekara 23 na yi aurena na farko. Sanin kanka ne cewa iyaye su ke yi wa mutum auren farko, amma ni ba haka ya faru ba domin kuwa mahaifina ya rasu. Saboda haka dole ta sa na sha gwagwarmaya na yi wa kaina aure. Na nemi wata yarinya da nufin in aure ta, amma sai ya zamana na fuskanci kalubale, domin iyayenta sun ce ba ni da komai da zan iya aurenta har ma in ci gaba da zama da ita. To amma kuma mahaifiyarta sai ta tambayi baban yarinyar, cewa a lokcin da ya aure ta me yake da shi? Wannan a 1970 ne lokacin da na yi auren farko. Kafin kuma mu yi auren abokin nemana ba yaro ba ne, amma ni ina kokarin yawan zuwa gidan su yarinyar kuma ina yin wasa da ’yan uwanta maza. Daga nan sai ta ce ita ba ta son wancan ni take so, amma ikon Allah bayan da muka yi aure da shekara 2 sai ta haihu kuma ta rasu. Bayan ta rasu ne sai na kara wani auren a watan Yunin 1975, a kuma watan Agusta sai muka tafi kasar Indiya don hutawa.

 Mutane suna yawan cewa ba ka cika yin magana ba, shin da gaske ne?

To me suke so in fada? Dole ne in kau da kaina daga wani abin, domin dole ne idan ka bude baki ka yi magana za a iya fassara ta da ma’ana daban-daban kuma a yi maka mummunar fahimta, tare da watsa jita-jita a tsakanin al’umma wanda zai iya haddasa husuma. To ni kuma ba na son abin da za a je ana rade-radi ko jita-jitar da za ta iya haddasa husuma. Don duk mutumin da ya zo zai kawo mini gulmar wani korarsa nake yi daga wurina.Kuma duk ma’aikatana da wadanda muke tare da su sun san ni da haka. Amma idan lokacin  da ya kamata in yi magana ce nakan yi maganar kuma nakan tara ’ya’yana mu yi hira da su, kuma su sun san cewa ba za su kawo mini wata gulma ba. Kuma muna wasanni tare da tafiya tare, kuma nan ba da dadewa ba za su ci gaba da tafiyar da harkokina. Don Mustafa wanda shi ne yake jagorantar rukunin injiniyoyi a masana’antata ta sarrafa man fetur, shi ne zai karbe ni, kuma ina da ’ya’ya 20, 12 mata 8 kuma maza. Wadansu muna aiki tare da su a yayin da wadansu kuma ba tare muke ba.

To shin za a iya cewa kamar kana da girman kai ne?

A’a ai girman kai abu ne wanda Allah ba Ya so a yi shi ga mutane, domin girman wani nau’i ne na siffofinSa. Kuma ni ba na da girman kai. Ni mutum ne mai saukin kai da walwala idan mutum ya fahimce ni.

To yaya kake daidaita kibarka?

A’a  abu na biyu da na dauka shi al’adata kuma kamar ya zama min ibada shi ne motsa jiki, domin ina motsa jiki tare da gudanar da wasanni irin na motsa jikin kamar su kwallon golf. Don ita ce mafi soyuwa a wasannina na motsa jiki, ina daukar hutun wata guda in fita waje, in yi ta motsa jiki da wasan golf, kuma ina jin dadin yin haka.

Wane abinci ka fi so?

A gaskiya na fi jin dadin cin abincinmu na gida irin su burabusko da tuwo miyar kuka, amma ban cika son cin shinkafa ba. Domin tun ina yaro ba na iya cin shinkafa ko kaza, na fi son in ci abincinmu na gargajiya.

Me kake ci idan ka yi tafiya kasashen waje?

Ina tafiya ne da kayayyakin abincina tare da wasu abubuwan da nake bukata

 Yaya kake gudanar da harkokin kasuwancinka na mai a Najeriya?

A yanzu na dawo  Legas, inda gudanar da taro da abokan huldata, domin mu ’yan kadan ne, to amma muna da girma ko fadi, na fada wa abokan huldata cewa ina yin wannan harka ce ba wai don in tara riba ba, ni dai ga nawa ina so in sanya wa kowa farin ciki ne, a ko’ina wannan shi ne burina. Muna biyan harajinmu, kuma na gode Allah domin ina da ingantattu kuma kwararrun ma’aikata wadanda na yarda da su kuma suka yarda da ni. Domin idan kana aiki a karkashin wani to kada ka yarda wata tababa ko taraddadi ko kokwanto ya shiga tsakaninka da shi. Amma dai babu wanda ya wuce kuskure don dukkanmu ’yan Adam ne, kuma duk abin da ya faru a masana’antata ina ganin ba wani abu ba ne kuma ba sai na je ba, komai za a iya warware shi cikin sauki.

Najeriya tana shigo da man fetur alhali ta cire tallafin man shin yana da kyau?

A’a wannan ba abin amincewa ba ne, ya kamata a daina ko kuma a rage shigowa da shi. Yaya za a yi a ce Najeriya tana shigo da man fetur? Daga shugabanni ne, ka dubi Dangote mana shi dai ba gwamnati ba ne amma yana kokarin kaddamar da matatar man fetur dinsa a badi, wannan mutum daya ke nan. To saboda me za a ce gwamnati ba za ta iya yi ita kadai ba? Mene ne cire tallafi? Ni ban yarda da cire tallafin ba wannan ai kashe kasa ce, shi ya sama a kullum muke ci baya maimakon ci gaba. Yanzu misali idan muka samu karfin wutar lantarki babu shakka za mu iya  kasancewa na 10, ko cikin sahun kasashe 10 masu karfin tattalin arziki a duniya, saboda ba ma bukatar mu rika rokon masu saka hannun jari a kasarmu su zo. Domin masu sanya hannun jari suna bukatar wutar lantarki da ingantattun hanyoyi to kuma muna da su za mu iya duk yin abin da za su iya yin mana a kasa. To amma ka ga abin ya faskara, ba mu da su yanzu ko a cikin kananan hukumomi 774 da muke da su a kasar nan ba su da isasshiyar wutar lantarki, ko ruwan sha. Wannan yana cikin damuwa, to ka ga ai wannan shi ne matsalar.

To yanzu ina mafita?

Babu wata mafita sai dai kuma addu’a, sannan ni ina ji mana baya gare mu yadda za su zo su tarar babu wani abu ingantacce. To amma ina sa ran cewa su za su iya gyarawa, amma kuma a yanzu sai mu gode Allah tunda yanzu Ya kawo mana Shugaba Muhammadu Buhari, wanda muke tsammanin zai iya fidda A’i daga cikin duma. Domin Allah ne Ya kawo shi duk da cewa wadansu mutane na kokarin yi masa zagon kasa, maimakon su yi masa addu’a, Allah Ya taikmake shi ya iya gyara kasar nan tare da ba shi hadin kai da goyon baya, Buhari ba mutum ne wanda zai yaudari mutane ba ko ya sace musu dukiya ba, ko ya yi ta fadin karya ba cikawa. Ina mamakin yadda Buhari ya kasance dan Siyasa, domin ni ba na sha’awar siyasa ganin ba zan iya tsayawa in fada wa mutane karya ba.

Shin akwai wata jam’iyyar siyasar da ta taba tuntubarka?

Eh, sun yi kokari a lokutan baya, amma ni ba na da sha’awar in shiga kowace jam’iyyar siyasa ce saboda ’yan siyasa za su fada maka duk abin da kake so ka ji ne, to amma kawai suna yi ne don su samu kuri’arka, kuri’arka kuma ’yancinka ne.

 Me ke dadada maka rai a rayuwa?

Eh, a gaskiya abin da nake jin dadinsa shi ne in taimaka wa al’umma, don taimaka wa al’umma yana sanya ni cikin farin ciki kwarai da gaske.