Da Dumi Dumi

Ban ga laifin kalaman Osinbajo ba – Buba Galadima

Injiniya Buba Galadima

Aminiya ta gana da Injiniya Buba Galadima, daya daga cikin mukarraban dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, dangane da kalaman Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, inda ya ce bai ga laifinsa ba:

 

An ruwaito Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo yana kira ga al’ummar Yarbawa su zabi Buhari a zabe mai zuwa don mulki ya koma yankinsu a shekarar 2023, me za ka ce?

To abu biyu ne. Na farko ’yan Najeriya ba sa tsayawa su yi nazari a kan abin da wani mutum ya fada ko wadansu mutane suka fadi. Osinbanjo shi ne Mataimakin Shugaban Kasa a yanzu, yana ci yana sha yana zaune a daki mai sanyi. Kodayake shi ma ya nuna mana cewa gwamnatinsu ta gaza samar da wutan lantarki don na gan shi yana yawo da na’urar cajin waya (Power bank) a hannunsa, duk da matsayinsa na Mataimakin Shugaban Kasa. Amma dai yana nadawa yana cirewa, yana kai ayyuka na alheri ga al’ummarsu da yankin Kudu maso Yamma da ya fito. Sannan  ya arzuta ’yan uwansa ko ma in ce wannan gwamnatin ta arzuta ’yan uwansa Yarabawa fiye da kowane jinsi a kasar nan, ciki har da Fulani da ake cewa Buhari na daya daga cikinsu. Kai ko lokacin da Obasanjo ya yi mulki ba su taba jin dadi irin lokacin wannan gwamnati ba. To mene ne laifinsa idan ya bukaci al’ummarsa su sake zabar gwamnatin don su ci gaba da jin dadi, a ci gaba da kawo musu abubuwan alheri wanda  wadanda suka zabi Buharin wato ’yan uwansa ba su samu ba? Ka ga ai bai da laifi kuma kowace jam’iyya tana da dabarun da ta tsara don jawo hankalin al’umma don cin zabe. Shi a ganinsa wannan abin da ya gaya musu ne zai kawo musu kuri’a. Mu a matsayinmu na ’yan adawa, mun yi maraba da abin da ya fada, domin ko ba komai idan ka raba Kudancin Najeriya kashi 3, Yarabawa na da kashi daya ne, kuma a nan din ma sai mun yi raba daidai da shi. Kuma baicin haka mu ma sai mu koma wajen yankin Ibo mu ce da su mun dauki naku, muna bukatar ku kada mana kuri’arku, don kuma da sauran al’ummar bangarorin Najeriya su ji dadi . Saboda a yanzu dan yankin Arewa ne ke mulki amma kahon ne kawai ya rika wadansu ne ke tatsa.

Sannan mu je bangaren Kudu maso Kudu, su ma mu gaya musu, ka ga mutuwar wani tashin wani. Saboda haka ban ga laifinsa ba idan ya fada wa al’ummarsa haka. Sai dai inda nake ganin laifin, shi ne dan uwanmu da muka zaba, muka yi dukan gwagwarmaya ta rayuwa don ganin ya yi nasara, sai ga shi ya fifita wata al’umma a kanmu, ya ki yi mana adalci. Idan aka zo rabon dukiyar kasa da ayyuka, mu yake zalunta. Mu mun sani da saninsa ake wadannan abubuwa duka, kuma idan har ya dawo wanda ba ma fata, idan ya gama na tabbatar maka su zai ba mulkin. Ka ga dai a yanzu mun ci yaki amma an bar mu da kuturun bawa. Hatta dan buhu 1 ko 2 da al’umma da ke zaune a kan iyaka za su shigo da shi don su samu ’yar Naira 500, yanzu an rufe. Da a yankin Yarabawa ne ya yi irin haka da yanzu duk duniya an ji su. Sai dai saboda mu ya raina, a yanzu ba barawo sai Bahaushe, sai Musulmi, sai dan Arewa, su kuwa can kowa sunansa Muhamman. Yanzu har akwai makabarta a Daura da ake kira makabartar Buhari, inda ake binne wadanda Kwastam suka harbe da zarar an gan su da buhun shinkafa ko guda daya. Saboda haka iya ruwa fid-da- kai, kila su a ganinsu wannan ne zai sa su ci zabe.

ADVERTISEMENT

Wace illa kake jin bayanin nasa zai iya jawo wa hadin kan al’ummar kasa?

Ina ruwan Buhari da hadin kan al’umman kasa? Ai shi abin da ya ga dama ake yi, shi ai ma’asumi ne saboda haka duk abin da ya ga ya yi daidai dole kowa ya dauka haka nan ya bi. Shi ya sa ma ba ya neman al’umma, ba ya yakin neman zabe, kuma koda za ka yi masa aikin ma sai ka je ka durkusa ka roke shi sannan ka je ka yi amfani da aljihunka. Kuma ko na gode ba zai ce maka ba. Shi ya sa koda ka yi ka gama ba ka isa ka ce duk wanda ya ci ladan kuturu sai ya yi masa aski ba.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya