Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ban karbi Naira miliyan 450 din Diezani ba saboda sun fi karfin motata – Balgore

Malam Muhammad Dele Belgore
Malam Muhammad Dele Belgore

Malam Muhammad Dele Belgore wanda Babban Lauyan Najeriya ne (SAN), ya musanta zargin da Hukumar EFCC ke yi masa na almundahanar Naira miliyan 450 a shekarar 2015.

Kafar labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito cewa Hukumar EFCC ta gurfanar da shi ne a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan zarginsa da karbar Naira miliyan 450 daga cikin Dala miliyan 115.01 da ake zargin tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur Diezani Alison-Madueke, ta rarraba don gudanar da kamfe din zaben shekarar 2015.

ADVERTISEMENT

Hukumar EFCC ta ce Balgore da tsohon Ministan Tsare-Tsare, Farfesa Abubakar Sulaiman, sun je ofishin bankin Fidelity Bank da ke Ilorin a ranar 26 ga Maris din 2015, domin su sanya hannu su karbi Naira miliyan 450.

Sai dai lokacin da yake bayar da shaida don kare kansa a ranar Litinin da ta gabata, Dele Balgore ya amince cewa manajan bankin ya gayyace shi a ranar 26 ga Maris din 2015 domin ya karbi Naira miliyan 450, amma ya ce ya bar bankin ba tare da kudin ba.

ADVERTISEMENT

Babban Lauyan wanda shi ne ko’odinetan kwamitin sake zaben tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a lokacin ya ce bai karbi kudin ba ne saboda lokacin da ya isa bankin ya fahimci kudin sun fi karfin motarsa kirar Jeep Toyota Prado.

Belgore ya ce: “Na fada wa shaidar mai kara na 1 (Manajan Bankin) cewa ba zan karbi kudin ba kuma na ba shi dalilai biyu. Na farko na ce kudin sun zo ne wuni biyu kafin zabe; kuma dukan masu ruwa-da-tsaki da ’ya’yan jam’iyya suna sane da zuwan kudin don haka ina ganin akwai hadari in dauki irin wannan dimbin kudi daga bankin a tsakiyar dare. Dalili na biyu shi ne ban zo shirin in karba tare da tafiya da wannan tulin kudi ba, domin na zo ne ni kadai a motata Toyota Prado. Kuma kamar yadda na fadi dazu, wannan tulin kudi da na gani a bankin akalla ya kai tsawon kafa uku zuwa hudu. Don haka na fada wa shaidar mai kara na daya cewa idan motar daukar kudi za ta dauko wannan kudi daga Babban Bankin Najeriya zuwa bankin Fidelity, babu yadda za a yi in iya daukar wannan kudi a motata Toyota Prado.”

Belgore ya ce sakamakon muhawarar da suka yi a tsakaninsu da Suleiman da manajan bankin ne, sai manajan bankin y a ce su sanya hannu kan sun karbi kudin, kuma ya amince a ajiye kudin a ma’ajiyar bankin. “Bayan sanya hannu a kan takardun, sai na bar bankin ba tare da kudin ba. Ban dauki ko kwabo ba; na bar bankin ne hannu fanko,” inji shi.

Alkalin Kotun Mai shari’a Rilwan Aikawa ya dage sauraron shari’ar zuwa 28 ga Fabrairun nan, bisa rokon lauyan Belgore, Mista Ebun Shofunde (SAN), wanda ya ce yana bukatar lokaci ya kali hoton kyamarar abin da ya gudana a harabar bankin a ranar 26 ga Maris din 2015, lokacin da Belgore da Suleiman suka je.

Hukumar EFCC ta ce Belgore da Suleiman sun amshi kudin ne alhali suna da ‘cikakkiyar masaniya’ cewa Naira miliyan 450 sun fito ne daga Diezani ta haramtacciyar hanya suka karkasa su ba tare da bin ka’idojin harkar kudi ba, wanda hakan ya saba wa dokar almundahanar kudi.

Mutanen biyu dai sun musanta zargin.