Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ban saki matata don za ta zabi Buhari ba – Abdullahi Yadau

Abdullahi Yadau da matarsa Fatima da ‘ya’yansu uku
Abdullahi Yadau da matarsa Fatima da ‘ya’yansu uku

Wani rahoto da ya tayar da kura a kwanakin baya da Sashin Hausa na gidan Rediyon BBC ya bayar cewa wani mutum mai suna Abdullahi Yadau da ke kauyen Unguwar Gero a Karamar Hukumar Kanam a Jihar Filato ya bugi matarsa, ya karya mata hakora biyu sannan ya sake ta, don ta ce Shugaba Muhammadu Buhari za ta zaba a zaben Shugaban Kasa mai zuwa, ya tabbata dai ba gaskiya ba ne.

A rahoton an ce matashin ya umarci matarsa ta zabi dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ne idan lokacin zaben ya zo, inda ita kuma ta bijire wa umarnin, al’amarin da aka ce ya kai ga saki har biyu bayan an ce ya lakada mata duka.

ADVERTISEMENT

Sai dai mijin matar mai shekara 32 ya karya labarin, inda ya ce shi dan ga-ni- kashe-nin Buhari ne, kuma yana son matarsa bai taba daga mata yatsa ba ballantana ya dake ta har a zo ga maganar saki.

Kurar da labarin ya tayar ne ya sanya jaridar Aminiya ta ziyarci kauyen Unguwar Gero da aka ce al’amarin ya faru don tantance sahihancin labarin.

ADVERTISEMENT

Sai dai a lokacin da Aminiya ta tattauna da Abdullahi Yadau da matarsa Fatima sun karyata labarin, inda suka ce suna zaune lafiya cikin kaunar juna.

Gidan Rediyon BBC ya rawaito wata murya a matsayin muryar Abdullahi Yadau da ke cewa ya saki matarsa ce saboda ta ce dole sai ta zabi Buhari alhali shi kuma ya umarce ta kan ta zabi Atiku, al’amarin da ya sanya ya sake ta saki biyu a gaban mahaifiyar matarsa.

Wannan lamari ya jefa mutanen kauyen Unguwar Gero da ke Gundumar Garga a Karamar Hukuma Kanam cikin kaduwa, inda suka nuna mamakinsu dangane da danyen aiki da mutum nagari kamar Abdullahi zai aikata na dukan matarsa kafin ya sake ta.

A lokacin da Aminiya ta tattauna da shi a gidansa a kauyen ya ce ya samu kansa kunci da takaici bayan rahoton da BBC ya watsa a kansa da matarsa.

Abdullahi wanda ya ce ba ya ma yarda a dora wa Baba Buhari laifi ya ce ya ji mamaki a ce ya umarci matarsa ta zabi Atiku a zabe mai zuwa.

Ya ce a dalilin labarin sai da ya yi gudun hijira daga gidansa saboda tsoron abin da zai je ya zo.

Aminiya ta gano cewa wani mutum mai suna Khamisu Maidankali ne ya hilaci BBC har suka yi rahoton, saboda lokaci zuwa lokaci, shi Maidankali yakan taimaka musu da labarai idan wani abu ya faru a kauyen Unguwar Gero da kewaye.

Wani dattijo a kauyen mai suna Abdullahi Ahmad ya ce “Maidankali yakan kira BBC ya ba su labari, domin ko lokacin da iska ta yaye rumfin dakunan mutane a kauyen nan shi ne ya ba BBC labarin kuma suka yi amfani da shi.”

Dattijon ya ce amma Maidankali yana da tabin hankali, wanda ya samu kimanin shekara 13 da suka gabata lokacin da ’yan fashi da makami a kan babura suka kashe mahaifinsa a gabansa.

Dattijon ya ce idan har mutum bai san Maidankali ba, ba zai taba zaton yana da tabin hankali ba, saboda ba koyaushe yake nunawa ba, babu mamaki BBC ba su san da haka ba.

A lokacin da Aminiya ta je gidan Abdullahi Yadau a kauyen ta iske matarsa Fatima tana yi wa daya daga cikin ’ya’yansu uku wanka kafin ta shirya shi don ya tafi makarantar firamare da dalibai ke karatu da rana.

Fatima ta ce ba ma sunanta Hafsat ba kamar yadda aka bayyana a rahoton na BBC.

Ta ce, “Sunana Fatima Abdullahi ba Hafsat ba, shekaruna 24, a gaskiya ban ji dadin labarin da aka yada a kanmu ba, wannan labari ba gaskiya ba ne, ba mu ma ji labarin a BBC ba, amma mutane da yawa sun ji kuma sun zo gidanmu don tantance sahihancin labarin.”

Ta ce, a yanzu aurensu ya kai shekara bakwai, kuma an shirya wannan rahoto ne don a bata musu suna, “Ni da mijina muna zaman lafiya kuma cikin farin ciki, babu wanda ya taba shiga tsakaninmu, bai kuma taba daga mini yatsa ba ballantana ya doke ni har ya karya mini hakora.”

Fatima wanda take sayar da kayan miya ta ce ta samu kanta cikin mamaki lokaci da ’yan uwa da abokan arziki suka cika mata gida dalilin wai an ji mijinta ya yi mata duka har ma da saki.

Ta ce, “Sun zo suna tambayar wai mijina ya yi mini saki biyu, kuma har ya yi mini duka dalilin na ce dole ni Buhari zan zaba, shi kuma ya ce dole in zabi Atiku?”

Fatima ta kuma karyata cewa dan uwanta mai suna Ibrahim ya yi magana da BBC, domin dan uwanta a yanzu ma yana zaune ne a Lafiya da ke Jihar Nasarawa, “Mun san wadanda suka sanar da BBC labarin, suna nan kauyenmu, har yanzu ban san dalilin da ya suka aikata wannan danyen aiki ba,” inji ta.

Abdulllahi Yadau mijin Fatima ya bayyana wa Aminiya cewa tunda abin ya faru a ranar Laraba makonni biyu da suka gabata sai da ya yi kwana uku bai yi wanka ba saboda halin zullumi da ya samu kansa a ciki.

Ya yi zargin cewa Khamisu Maidankali wanda yake ba BBC labarai ne ya kitsa duk abin da ya faru, inda ya hada baki da wani mutum da ake kira Hamisu wajen aiwatar da nufinsu.

“Hamisu shi ne ya yi magana a matsayin ni, inda Khamisu Maidankali ya yi magana a matsayin yayan matata. Mun iya gane muryoyinsu ne saboda muna tare da su a wannan kauye,” inji shi.

Da Aminiya ta tambaye shi ko me ya sa suka zabi yin amfani da sunansa wajen shirya wannan al’amari, sai ya ce, “Muna da majalisa da muke zama inda a nan muke tattauna al’amuran yau da kullum, a ranar Larabar da abin ya faru misali karfe 1:30 na ranar muna tattaunawa ne a kan zaben Shugaban Kasa. Sai na ce zai yi kyau a yi labari makamancin irin wannan a Intanet don a ji ra’ayin jama’a, sai Khamisu Maidankali ya ce, a’a a yi amfani da rediyo zai fi dacewa da kuma jan hankali, sannan ya ce a yi amfani da BBC. Jim kadan na bar majalisar shi ne ya zo wurina ya ce mu kira BBC, sai na ce masa, a’a, wasa ne kawai. Sai ya tafi bai ce min komai ba, daga baya ya sake zuwa wurina a kan mu sake kiran BBC sai na ki yarda, inda na hau babur dina na ta fi wani kauye mai suna Gajin-Duguri da ke Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi da bai fi tafiyar minti 10 a kafa daga kauyenmu ba,” inji Abdullahi Yadau.

Ya ce, “A wannan ranar Larabar bai sani ba ashe Maindankali ya samu wani suka hau bishiyar kuka da suke samun network (sadarwar waya), sai suka kira BBC inda Maidankali ya ce shi ne Ibrahim Suleiman yayan matata, shi kuma Hamisu ya yi magana a matsayin ni ne.”

Abdullahi ya ce bai saurari shirin BBC na ranar ba saboda rediyonsa ya lalace, kawai sai ya kwanta barci, kuma washegari da sassafe sai kanensa ya zo gida ya same shi don ya ji bahasin dalilin da ya sa ya doki matarsa, ya kuma sake ta don bambancin siyasa, amma ya sanar da shi ba haka ba ne. Ya kama hannunsa ya kai shi wurin matarsa da ke cikin daki.

Ya ce, mutane sun yi ta zuwa gidansa ciki har ma da mahaifiyar matarsa da ta zo don tambayar abin da yake faruwa.

Ya ce, abin da ya kara tsorata shi har ya gudu ya bar gida shi ne yadda ’yan sanda suka zo nemansa gida har sau biyu.

Ya ce, ’yan sanda sun zo kauyensu sau biyu, “Na farko da misalin karfe 1:00 na ranar Alhamis, sannan suka sake dawowa da misalin karfe 2:00 na daren ranar, kafin su zo da ma na samu jita-jitar cewa Gwamnan Jihar Filato ya sa ’yan sanda su kama ni. Don haka da na ji jiniyar jami’an tsaro sai na tsorata na gudu. Ashe sun zo wurin dagacin garinmu ne inda bayan ya sanar da su abin da yake faruwa sai suka ce sai sun ga matata, sun je wurinta sannan sun dauki hotunanta kafin suka tafi,” inji shi.

A ranar Alhamis din ne suka sake dawowa da misalin karfe 2:00 na dare bayan tuni Abdullahi ya tsere zuwa kauyen Gajin-Duguri tsoron ko za su kama shi, inda bayan ya dawo gida sai aka ce ai ’yan sanda sun tafi da matarsa ofishinsu da ke Dengi a Karamar Hukumar Kanam.

“A washegarin Juma’ar ne sai na je ofishin ’yan sandan tunda sun riga sun tafi da matata, inda suka yi mini wasu tambayoyi a kan ko na daki matata kamar yadda rahoton BBC ya rawaito, amma a karshe dai suka gane ba ni da laifi kuma ban bugi matata ba, shi ne suka bar mu muka tafi,” inji Yadau.

Ya ce a yanzu ya fara samun natsuwa tunda gaskiya ta fito har an fahimci labarin da aka watsa din na karya ne.

Abdullahi ya ce shi masoyin Baba Buhari ne duk da cewa an yanzu ba ya samun kudi kamar kafin Buhari ya hau mulki, amma zaman lafiya da tsaron da aka samu ya sanya yana ci gaba da kara son Buhari, kuma ko da matarsa tana da ra’ayin wani dan takara da ya saba da nasa ba zai hana ta ba saboda tana da ’yancin haka domin siyasa ce.

Abdullahi ya karya jita-jitar da ake yadawa cewa wai dole aka sa matarsa ta aure shi, “Ina son matata, ita ma tana sona, wannan duk jita-jita ake yadawa, ina so mutane su sani mun yi soyayya sosai kafin mu yi aure,” inji shi.