Da Dumi Dumi

Ban samu takardar tsigewa ba – Shugaba

Shugaban Karamar Hukumar Zariya Injiniya Aliyu Idris Ibrahim
Shugaban Karamar Hukumar Zariya Injiniya Aliyu Idris Ibrahim

Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Injiniya Aliyu Idris Ibrahim Magani Sai-Da- Gwaji ya ce bai samu takardar da ake cewa kansiloli sun tsige shi daga kujerarsa ba.

A taron manema labarai da ya kira, Mai ba Shugaban Karamar Hukumar Shawara Kan Harkokin Watsa Labarai da Sadarwa Alhaji Abubakar Rilwan ya bayyana cewa har lokacin da yake tattaunawa da manema labarai ba su ga wannan takarda ba.

Alhaji Abubakar Rilwan ya ce a iya saninsu kansilolin ba su yi zama ba a ranar Laraba, sannan ya ce “Za su zauna ne ba akawun majalisa kuma ba sandar majalisa?”

A cewarsa wannan zama bai da bambanci da zaman shan shayi saboda rashin bin ka’idar tsige zababben Shugaban Karamar Hukuma kamar yadda dokokin tafiyar da kananan hukumomi ta Jihar Kaduna suka tanada.

Ya ce zargin rashin bin kai’dojin bayar da kwangiloli da kansilolin suka yi babu kanshin gaskiya a ciki, “Sun manta ne da su ake zama, tare da ba su kwafin abin da aka tattauna don aiwatarwa?”

ADVERTISEMENT

Haka kuma kan maganar almubazzaranci da kudin al’umma, Rilwan ya ce a shirye suke a zo a yi ’yar kure domin suna da dukkan bayanan yadda kudaden karamar hukumar ke tafiya.

Sai kuma zargin rashin zaman lafiya da su kansilolin da kuma mahukunta da ke aiki da shi, a nan ma ya ce akwai kyakkyawar dangantaka ta aiki da duk wani ma’aikaci ko wadanda suka yi zabe.

A ranar Larabar makon jiya ce kansilolin Karamar Hukumar Zariya, a karkashin jagorancin Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Kansilolin Alhaji Akilu Abubakar suka kira taron manema labarai tare da raba musu takarda mai dauke da sa hannun kansiloli goma da ke nuna cewa sun tsige Shugaban Karamar Hukumar Zariya Injiniya Aliyu Idris Ibrahim Magani Sai-Da Gwaji daga kujerarsa, tare da bayyana cewa sun dauki matakin farko, har sun mika wa Akawun Karamar Hukuma takardar.

Sai dai Shugaban Karamar Hukumar ya garzaya kotu domin neman ta dakatar da yunkurin da kansilolin ke yi na tsige shi.

Kamar yadda wata takarda da kansilolin suka kara nuna wa manema labarai ke cewa, duk da wannan takarda ta kotu da suka samu ai su ma wata dama ce da tsarin mulki ya ba su, kuma shi suke bi don haka ba za su kauce wa doka ba.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya