Da Dumi Dumi

Ban taba tsammanin zan buga wa Manchester United wasa ba – Ighalo

Dan kwallon Najeriya Odion Ighalo ya ce bai taba tsammanin burin da yake da shi lokacin yana yaro na buga wa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kasar Ingila kwallo zai cika ba.

Kungiyar Manchester United ta karbo  Ighalo a matsayin aro ne daga kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua ta kasarChina a watan Janairun bana.

Kocin Kungiyar Mnachester, Ole Gunnar Solskjaer ya tsaida matsayarsa ta sayen Ighalo mai shekara 30 ganin yadda kungiyar take da matsalar dan wasan tsakiya wanda kuma zai iya taimakawa wajen kai farmaki.

Tsohon dan wasan Watford ya samu yabo da fatar alheri da yawa bayan da ya koma Man U., da buga wasa. Haka kuma Ole Gunnar ya bayyana cewa idan har Ighalo ya ci gaba da buga irin wasan da suke son ganin yana bugawa, kungiyar za ta iya sayensa.

Ighalo ya bayyana cewa yana jin dadin zama da kungiyar ta Manchester United amma bai taba tsammanin hakarsa za ta kai gaci ba ta buga mata wasa.

ADVERTISEMENT

“Idan kana cewa kana son ka buga wa Kungiyar Manchester United wasa a lokacin da muke yara sai ka ji mutane na cewa ‘kai ba ka da hankali ne?’ Domin a waccan lokacin ba ka ma zaton abin mai yiyuwa ne,” Ighalo ya fada wa beIN Sports.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya