Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ban taba tunanin zama Gwamna ba – Bindow

Gwamnan Jihar Adamawa, Sanata Jibrilla Bindow ya  ce daidai da rana daya bai taba mafarkin zai zama Gwamnan jiharsa ba.

Gwamna Bindo ya bayyana haka ne yayin taron cika shekara 35 da kafa kungiyar tsoffin Daliban Makarantar Sakandaren Kimiyya da ke Miyango wanda ya gudana a otal din Three Angels Apartment da ke Rayfield a Jos a karshen makon jiya.

ADVERTISEMENT

Ya ce, “Ni ba dan siyasa ba ne, amma na koyi siyasa a rayuwata, mutane da yawa sun san ba ni da burin yin siyasa domin siyasa ba ta yi ba, ban taba mafarki daidai da rana daya in shiga siyasa har in zama Gwamna ba, amma yanzu Allah Ya kaddara na zama Gwamna.”

Gwamna Bindow ya ce duk da cewa Allah Ya zama ya zama Gwamna, hakan ba yana nufin cewa ya zama Gwamna ba tare da ya shirya ba ne.

ADVERTISEMENT

“Ina so mutane su sani ban zama Gwamna ba sai da na yi shiri, domin na koyi siyasa a wurin ’yan siyasa masu yawa,” inji shi.

Gwamnan ya shawarci mutane  cewa idan har sun samu wani mukami, to su yi mulki ba tare da nuna son kansu ba, domin hakan ne zai sa a samu ci gaba mai dorewa.

Ya ce, “Idan Allah Ya ba ka mukami sai ka gudanar da ayyukanka ba tare da nuna son kai ba, hakan nake yi a Jihar Adamawa, inda a yanzu ake samun ci gaba.”

Gwamna Bindow ya ce, “A lokacin da aka zabe ni Gwamna a shekarar 2015, Jihar Adamawa na cikin jihohin da suke da koma baya, amma sakamakon ayyukan da na gabatar yanzu jihar tana sahun gaba wajen samun ayyukan raya kasa da kuma masu samar da walwalar jama’a.”