✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bana a saki sak a kama cancanta

A halin yanzu dai saura kwana takwas a gudanar da zaben Shugaban Kasa wanda ya sanya jam’iyyun siyasa kara himmatuwa wajen yakin neman zabe domin samun…

A halin yanzu dai saura kwana takwas a gudanar da zaben Shugaban Kasa wanda ya sanya jam’iyyun siyasa kara himmatuwa wajen yakin neman zabe domin samun nasara a zaben da za a yi ranar Asabar 16 ga wannan wata na Fabrairu.

A yayin yakin neman zaben da ake gudanarwa shugabanni da kuma ’yan takara na manyan jam’iyyun kasar nan wato APC da PDP suna ta yin kira ga magoya bayansu da su zabi ’yan takarar jam’iyyun nasu ‘daga sama har kasa, kuma daga kasa har sama.’ Wato suna so a bi tsarin nan na sak ke nan da aka yi amfani da shi a zabubbukan da suka gabata.

Sai dai kuma wannan tsari na sak ba abu ne da ya kamata masu zabe su yi amfani da shi ba a wannan karon domin a zaben shekarar 2015 an yi amfani da shi sau-da-kafa amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

A zaben shekarar 2015 Jam’iyyar APC ta bukaci magoya bayanta su yi APC sak da nufin samun Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Tarayya, domin kuma gwamnoni su samu ’yan majalisa a jihohinsu yadda ’ya’yan APC za su zama masu rinjaye a majalisun.

Babu shakka an samu hakan, domin Jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a Majalisar Tarayya, sai dai kuma abin da aka so bai samu ba, domin ba a samu kyakkyawar jituwa ba a tsakanin bangaren shugaban kasa da bangaren majalisa ba.

Hujjar da ake bayarwa ta yi sak ita ce, idan jam’iyya guda ta samu shugabanci a Bangaren Zartarwa da Bangaren Majalisa ba za a samu matsala ba wajen aiwatar da ayyuka, domin ana samun matsala ce idan jam’iyyar adawa ta kasance tana da katabus a majalisa, saboda za ta zama tarnaki ga Bangaren Zartarwa.

Baya ga matsalar da aka samu tsakanin Bangaren Zartarwa da Bangaren Majalisa a matakin tarayya wanda hakan ya jawo matsala wajen aiwatar da kasafin kudi da kuma amincewa da wasu dokoki da jam’iyya mai mulki take so, tsarin sak kuma ya kwashi mutanen da ba su cancanta ba, ya maka su a cikin Majalisar Tarayya, musamman wadanda suka tafi majalisun daga yankin Arewacin kasar nan, domin wadansu sun je majalisun ne domin su dumama kujera kawai saboda ba su san abin da ya kai su wurin ba, guguwa ce kawai ta kwashe su ta jefa a majalisun, bayan sun kayar da ’yan takara kwararru  da ya kamata su je a yi gwagwagwa da su a majalisun.

Akwai ’yan takara nagari wadanda ya kamata a ce su ne aka zabe su saboda cancantarsu amma saboda banbamcin jam’iyya sai aka zabi wadanda ba su dace ba aka bar su saboda tsarin sak da aka yi amfani da shi.

Saboda haka ya kamata al’ummar yankin Arewacin kasar nan su fahimci cewa ba kowa ne za a zaba ya tafi majalisa ba, dole ne a rika la’akari da cancanta domin wuri ne da ake yin dokokin da za su shafi rayuwarmu ta yau da kullum, idan ba a samu wakilai kwararru ba za a samu matsala domin za a yi ta samun dokokin da za su cutar da yankin Arewa saboda an tura wakilan da ba san inda aka nufa ba balle har su tashi a majalisa su bayar da gudunmawarsu a muhawarar da ake yi game da wani al’amari da ya taso.

Yanzu ba a yin jam’iyya saboda akida sai don neman mukami, shi ya sanya ’yan takara suke tsalle-tsalle daga wannan jam’iyya zuwa wancan domin samun biyan bukatarsu. Idan kuma dan takara ya bar jam’iyyarsa ya koma wata sai kuma bai samu abin da yake nema a can ba sai ya sake komawa jam’iyyar da ya bari matukar an yi masa albishir da samun tsayawa takarar.

Domin haka babu wani amfani da tsarin sak yake haifarwa sai matsala kawai domin yana sanyawa a zabi mutanen da ba su dace ba a bar wadanda suka dace, kuma yin sak da ake yi da nufin samun hadin kai a tsakanin Bangaren Zartarwa da Bangaren Majalisa ba ya samuwa, domin haka gara a bi cancanta wajen zaben ’yan takara maimakon la’akari da jam’iyyar da suke ciki.

Dan takara nagari shi ya kamata a zaba a kowace jam’iyya yake, ta haka ne kawai za a samu shugabanni nagari masu kishin talakawa ba masu kishin aljihunsu ba.

Ga dukan alamu mutane da dama sun fahimci illar bin tsarin sak da aka yi a baya saboda haka a wannan karon muna fata za su gyara kuskurensu su yi zabe ta hanyar la’akari da cancanta ba jam’iyyar da dan takara ya fito ba. A daure a saki sak a kama cancanta.