✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bana farashin dabbobi ba yabo ba fallasa

A yayin da gobe za a gudanar da bukukuwan babban sallah da ya kunshi yin layya da dabbobi, a bana farashin dabbobin sun kasance ba…

A yayin da gobe za a gudanar da bukukuwan babban sallah da ya kunshi yin layya da dabbobi, a bana farashin dabbobin sun kasance ba yabo ba fallasa.
Aminiya ta ziyarci Kasuwar Zango da ke Tudun Wada Kaduna, wadda aka kafa ta fiye da shekara 47 da suka wuce kuma tana daya daga cikin manyan kasuwannin dabbobi a yankin arewacin kasar nan, inda Alhaji Bukar Aliyu ma’ajin kungiyar ’yan kasuwar Zango ya ce: “A duk lokacin bukukuwan Babbar Sallah ana sayar da raguna akalla guda 50,000. Muna samun ragunar ne daga wurare kamar su: Nijar da Jigawa da Yobe da Katsina da yawancin garuwawan da ke iyaka da kasar Nijar.”
Ya ce, “a bara masu raguna asara suka yi domin rashin biyan albashi a kan kari da gwamnati ba ta yi ba. Hakan ya sa ga raguna da dama, amma ba masaya. A wancan lokacin farashin karamin rago ba ya wuce Naira 11,000, amma a karshe sai da aka yi kwantan fiye da guda 5,000. A bana kuwa farashin karamin rago yana farawa ne daga Naira 13,000, amma ya zuwa yanzu kashi biyu cikin uku na ragunar da ke wannan kasuwar an yi masu lamba, wato an saye su, sai dai kawai ranar Jajiberi ko ranar Sallah su zo su dauki kayansu. Idan mutane suka ga raguna birjik  za su yi zaton duka na sayarwa ne, amma ba haka ba ne. A gaskiya an samu ci gaba sosai idan aka kwatanta kasuwar bana da ta bara. Misali wanda yake sayo raguna 10 a bara, a bana shi ne mai sayo 15 kuma ya sayar cikin  kwana uku, ya koma ya kara sayo wasu. Ni kaina na sayar da ragon Naira 160,000”
“Wasu na ganin saboda zaben badi ne kasuwar ta bunkasa, amma ni ba ni da irin wannan tunanin. Dalilina kuwa  shi ne ’yan siyasa alkawari ne ba cikawa. Za su zo kamar da gaske za su siya a karshe sai ka neme su ka rasa. Akwai masu halin da za ka ga sun zo, sun sayi rago biyar zuwa shida, a gaskiya ban taba ganin wani dan siyasa da ya zo kasuwar nan ya sayi raguna don raba wa jama’a ba. Idan ma hakan na faruwa to ba nan ba ne.”
Wani magidanci mai suna, Abubakar Paki, wanda duk shekara yake zuwa kasuwar don sayen ragon layya, ya bayyana wa wakilinmu cewa: “A gaskiya akwai  raguna kuma suna da sauki sosai. Kodayake manyan raguna sun yi karanci. Wannan ya sa farashinsu yin sama. Amma idan aka kwatanta bara da bana za a iya cewa bana ba raguna sosai saboda matsalar tsaro. Ka ga kamar yankin gabashin kasar nan wanda ake shigo da raguna da dama daga can, hakan a yanzu ba ya yiwuwa kamar yadda aka saba saboda barazanar tsaro.”
Daga Kano kuma wakilinmu ya ziyarci wadansu kasuwannin jihar Kano, inda a kasuwar Badume da ke karamar hukumar Bichi, ya ruwaito cewa an sayar da raguna manya kan kudi Naira dubu 30 zuwa dubu 35,  inda kuma aka sayar da matsakaita kan Naira dubu 12 zuwa dubu 15. Sannan an sayar da  awaki manya kan kudi  Naira 4 zuwa dubu 6  zuwa dubu 8.
A kasuwar Gyaranya da ke karamar hukumar Minjibir, an sayar da manyan raguna daga Naira dubu  27  zuwa dubu  35, kana an sayar da  awaki daga Naira  dubu  7  zuwa dubu 10.
A kasuwar dambatta  inda ake sayar da shanu har da rakuma, farashin manyan shanu turkakku ya fara daga Nairu dubu  150 ne zuwa  dubu 250, inda aka rika sayar da rakuma daga Naira dubu 120 zuwa dubu 150.
Kazar gidan gona babba ana sayarwa Naira dubu zuwa dubu da 200, amma kajin gida ba sa wuce Naira 700 zuwa Naira dubu . Zabi kuma ana samunsu daga Naira dubu 1 da 500, talo-talo daga Naira dubu 5 zuwa dubu 7,  ya danganta da girmansa.
A cikin birnin Kano ko’ina aka duba idan da dan fili za a ga an kafa turaku an daure raguna ana sayarwa, kuma ana samun rangwame fiye da a lokutan baya ,sai dai  mafiya yawan mutanen da  Aminiya ta tattauna da su sun danganta rashin tsadar dabbobin da  rashin biyan albashi a makon da ya gabata, da kuma yanayin tattalin arzikin kasa.
Daga Kalaba kuma Wakilinmu ya ruwaito cewa, matsalar tsaro da rashin zama lafiya da ake fama da shi a wadansu jihohin  arewa maso gabashin kasar nan ya haifar da karancin dabbobin layya, musamman ma rufe kan iyakar Najeriya da Kamaru da aka yi, wanda ya sanya dabbobin suka yi karanci a kasuwar awaki ta Kalaba. Kamar yadda Alhaji Isiyaka Muhammad Hadeja, shugaban kasuwar awaki ta jihar Kuros riba   ya bayyana  wa Aminiya.  
Alhaji Muhammad Hadeja ya ci gaba da cewa, ‘’dabbobin da muka samu daga jahohin Jigawa da Kano zuwa makwabtan jahohi ne muka kawo nan . Mafi tsada daga Naira dubu 60 ne ,yayin da mafi kankanta ake samu a Naira dubu 15”.inji shi
Duk da mutane na fama da karancin kudi amma suna zuwa suna tayawa su koma.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci kasuwar akwai raguna da yawan gaske kuma mutane na zuwa saye, sai dai akasarin wadanda aka tattauna da su sun yi bayanin cewa rashin isassun kudi a hannu ya sanya za su jira har sai an samu rangwame.