Search
Subscribe
Bana za a samu karancin alkama a Kano – Manoma

Bana za a samu karancin alkama a Kano – Manoma

Manoman alkama a Jihar Kano sun ce akwai yiyuwar a samu karancin alkama a jihar a bana, sakamakon  wasu matsaloli da suka shafi rashin samun isasshen ruwa da kuma  jinkirin da aka samu wajen samun kayan noma da kuma rashin samun tallafi daga Babban Bankin Najeriya a karkashin shirin bashin noma.

Aminiya ta gano cewa an dade manoman alkama a jihar suna korafin cewa an bar su a baya game da rashin samun tallafi  daga cibiyar bincike ta Tafkin Chadi  wacce ke da alhakin kula da harkar noman alkama.

Wani manomin alkama mai suna Bahago Bello Gafan da ke Karamar Hukumar Garun Malam, ya ce fiye da shekara uku ke nan manoman alkama suna fuskantar matsalar neman iri kasancewar babu wata hukuma da ke samar musu da iri.

“Akwai lokacin da masu sarrafa alkama suke ba manoman alkama iri bayan Cibiyar Tafkin Chadi ta daina. Sai dai a yanzu ana bar manoman alkamar su nemi iri da kansu. A yanzu ma da Babban Bankin Najeriya yake bayar da tallafin ana samun jinkiri wajen samun irin, wanda hakan ya zame mana matsala saboda ita alkama tana da lokacin da ake shukarta wanda dole sai an bi shi, sau-da- kafa,” inji shi.

Idan za a iya tunawa wani lokaci a watan Satumban bara  manoman alkama a karkashin jagorancin Kungiyar Manoman Alkama ta Kasa sun koka game da jinkirin rabo da kuma samun tallafin bashin noma na iri da taki da kungiyar ta ce su ne suke damun harkar noman alkama a wannan lokaci.

Shugaban Kungiyar ta Kasa, Alhaji Salim Muhamamd ne ya bayyana haka a lokacin da aka yi  taron horarwa a bara, wanda Cibiyar Bincike ta Tafkin Chadi da sauran hukumomi da ke da ruwa- da-tsaki a harkar noman alkama suka shirya a Kano.

A cewarsa alkama tana da lokaci wanda kuma kowane manomi ya kamata ya kula da shi. Ya ce idan aka samu jinkiri a lokacin shuka to hakan zai shafi amfanin gonar; domin ba za a samu amfani mai yawa ba. Idan kuma aka yi rashin sa’a za a iya yin hasara gaba daya.

Ya bayyana takaicinsa duk da cewa ana samun tallafi daga Bankin CBN, amma har yanzu manoman alkama suna fuskantar matsala wajen samun kayayyakin noma.

“Ya zama wajibi mu yi kira ga hukumomin da suka kamata su tabbatar cewa dukkan tallafin da ake bayarwa ya isa ga manoman alkama a kan lokaci ko mu ci gaba da yin aiki muna samun ’yar ribar da ba ta kai ta kawo ba ko kuma ma mu rasa gaba daya,” inji shi.

Akwai tallafi daban-daban da ake ba wa noman alkama da suka hada da yin amfani da sabuwar hanyar noma ta zamani ta yin amfani da injin da yake yin kunya tare da yin shuka a lokaci guda. Wannan hanyar  ita ce take maganin duk wata illa da akan iya samu a gonakin alkama sakamkaon amfani da ruwa mai yawa.

Binciken Aminya ya gano cewa duk da wadanann matakai da manoman ke dauka da kuma hukumomin da ke kula da harkar noman alkama za su iya zamowa dan kadan a bana domin duk da cewa lokacin yin shuka ya karato amma hanyoyin ruwa na noman rani na Kadawa suna rufe wadda kuma ita ce babbar cibiyar da ke ba gonakin alkama ruwa a Jihar Kano.

Mai kula da harkar ruwan wato Hukumar Kogin Hadeja da Jama’are ta sanar cewa tana gyare-gyare ne wanda hakan ya janyo aka rufe hanyoyin ruwan. Galibin manoma musamman na alkama suna ganin an yi abin a lokacin da bai dace ba kasancewar ya hadu da lokacin da ake shukar alkama.

Bincike ya nuna cewa Cibiyar Bincike ta Tafkin Chadi ta mayar da wasu gonakin gwajinta na Kadawa zuwa Jihar Kaduna sakamakon rufe hanyoyin ruwan da aka yi inda manoma da yawa ke kallon hakan ya shafi harkar noman alkama a yankin.

Rufe hanyoyin ruwan ya ci karo da lokacin shuka wanda hakan ya tilasta yawancin manoman alkama suka ajiye batun noman a gefe. Haka kuma kimanin kashi 60 na manoman alkamar wadanda suke noma a Kadawa ba su yi shuka ba, saboda halin da suka tsnici kansu a ciki.

A cewar Alhaji Musa Dan Bala Garun Babba ya ce manoman da suka yi noman a wannan yanayin duk da rashin ruwa suna fuskantar matsalolin rashin girman shuka da sauransu. “Yawancinmu mun yanke shawarar kin yin shuka a bara saboda ba a samu ruwa ba sai a watan Disamba. Ita kuma alkama ana fara shukarta ce tun a watan Oktoba zuwa Nuwamba, hakan ya sa muka ki shuka don gudun tafka hasara. Amma a hakan wadansu sun yi shukar sai dai rashin ruwan ya shafi abin da suka shuka. Kuma duk da cewa an samu tsawon lokacin sanyi, amma ina tabbatar muku cewa a bana Jihar Kano za a samu karancin alkama,” inji shi.

Sai dai a wurin noman rani na garin Bagwai, manoman alkamar ba su hadu da wani tasgaro ba kasancewar karancin ruwan bai shafe su ba, kamar yadda Alhaji Danliti Bichi ya bayyana, inda ya ce a wajensu manoman alkama za su dara a bana domin za su samu amfani sosai saboda sun samu yanayi mai kyau da alkamar ke bukata.

“Duk da cewa noman da muke yi a nan bai kai na Kadawa ba; amma alkama a nan ba ta samu matsala ba saboda mun samu kyawun yanayi. Sai dai lura da yawancinmu ba mu samu tallafin gwamnati ba, amma duk da haka muna sa ran samun amfani mai yawa a bana. Idan ma na samu yadda nake so badi zan rubanya yawan abin da na shuka a bana,” inji manomin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin