✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Banki ya yi kuskuren tura wa wata sama da Naira biliyan 13 a asusunta

Wata mata da ke a Arewacin Jihar Tedas a Amurka  ta zama biloniya ta kwana daya bayan da bankin da take ajiyar kudi ya yi…

Wata mata da ke a Arewacin Jihar Tedas a Amurka  ta zama biloniya ta kwana daya bayan da bankin da take ajiyar kudi ya yi kuskuren tura mata makudan kudi a asusunta.

Matar mai suna Ruth Balloon, bayan da ta tashi daga aiki ta yi yunkurin duba asusunta don ganin kudin da suka rage a ciki, a bankinta na Legacy Tedas. Abin mamaki sai ta ga zunzurutun kudi Dala miliyan 37 (daidai da Naira biliyan 13 da miliyan 412 da dubu 500).

“Na yi mamaki matuka, har na ce lallai na zama mai kudi!” inji ta yayin da take magana da kafar labarai ta KTBT.

Bayan ta dan numfasa sai ta bayyana wa mijinta al’amarin da ke faruwa, inda ya nemi ta sanar da bankinta game da abin da ya faru. Ya ce ta tambayi bankin kan ko kudin ita ake nufin bai mawa, wanda a tunani zai iya zama gaskiya.

Balloon, ta tuntubi bankinta inda suka bayyana mata cewa an samu kuskure ne wajen tura kudin, kuma ba ita aka nufi tura mawa ba. Daga bisani bankin ya nemi afuwarta kuma aka kwashe kudin daga asusunta.

“Na so a ce wani ne ya ba mu kyautar wannan makudan kudi,” inji Balloon.

A wannan dan kankanen lokaci da Balloon ta zama biloniya, ta yi tsare-tsaren yadda za ta kashe wadannan kudi.

“Da farko dai ina so in yi tunanin yadda zan kashe kashi goma daga ciki, sannan zan bada tallafin wasu daga cikin kudin. Sannan zan sa hannun jari a cikin harkokin gine-gine,” inji ta.

Bankin Legacy Tedas ya fitar da sanarwa cewa tuni sun riga sun gyara kuskuren, kuma ba don Balloon ta yi kokari ba da za su gano kuskuren yayin gudanar da aikin dare.

“A ranar Talata, 10 ga Disamban da ya gabata, daya daga cikin masu ajiya a bankin ta yi ajiyar kudaden kasar waje a bankin, amma sakamakon hawa da sauka da shiga da fitar da kudaden waje ya sa bankin baya shigar da su kai-tsaya. Yayin da aka shigar da kudin, ma’aikatanmu sun yi kuskuren lambar asusun inda suka sa ta Balloon, hakan ya sa kudaden suka shiga asusunta,” kamar yadda bankin ya bayyan awa KTBT.

Balloon, ta ce ba ta da niyyar kin bayyana shigar kudin cikin asusunta, sai dai ta bukaci bankin ya yi mata godiya bisa kokarinta na sanar da su halin da ake ciki, da kuma kasancewarta mai hulda da banki tagari.

“Ko yanzu zan yi alfahari da cewa na taba zama biloniya ta kwana daya, kuma na dauki hoton shigowar kudin zan adana domin ya zama tarihi,” inji Balloon.