✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bankin CBN ya bayar da lasisi ga wani sabon bankin Musulunci

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar da lasisi ga wani sabon bankin Musulunci mai suna TAJ Bank Limited. Kafar labarai ta hausa.legit ta ruwaito jaridar…

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar da lasisi ga wani sabon bankin Musulunci mai suna TAJ Bank Limited.

Kafar labarai ta hausa.legit ta ruwaito jaridar Iwitness tana cewa Bankin CBN ya bayar da lasisin fara aiki ga sabon bankin Musuluncin ne a wata wasika da ya aike wa bankin a ranar Litinin da ta gabata, sakamakon gamsuwa da ya yi da cika dukkan sharuddan da Bankin CBN ya gindaya masa.

Sai dai Bankin CBN ya iyakance ayyukan Bankin TAJ a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Najeriya, tare da ba shi damar samar da babban ofishinsa a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Wannan ci gaba da aka samu a harkar cinikayyar kasuwanci irin ta Musulunci ta kawo adadin bankunan Musulunci a Najeriya sun zama biyu baya ga bankin Musulunci na Jaiz da aka kafa shekarar 2011.

Idan za a tun a shekarar 2003 aka fara haihuwar Jaiz a matsayin cibiyar hada-hadar cinikayya ta Musulunci da ba ta tu’ammali da riba, yayin da a shekarar 2011 Bankin CBN ya ba ta lasisin fara aiki a Arewa, da haka cibiyar ta zama bankin Musulunci na farko a Najeriya.

Bankin Musulunci na JAIZ bai fara aiki ba sai a ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2012, inda bayan samun karbuwa ya nemi izinin Bankin CBN ya ba shi dama ya fadada ayyukansu zuwa sauran sassan Najeriya,inda a shekarar 2016 Bankin CBN ya ba shi lasisin aiki a dukkan sassan Najeriya.