Da Dumi Dumi

Bankin DBN ya ba masu kananan masana’antu rancen Naira biliyan 100

Bankin Raya Kasa na Najeriya (DBN), ya ce a bana ya bada rancen Naira biliyan 100 ga masu kanana da matsakaitan masana’antu su dubu 95.

A wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa ta ce Manajan Daraktan Bankin DBN, Mista Tony Okpanachi, ya ce an bayar da basussukan ne ga kanana da matsakaitan masana’antu domin a  inganta su a kasar nan.

Ya yi wannan jawabi ne a ranar Talata a Maiduguri, yayin da yake jawabi ga mahalarta ‘Taron Yadda Za a Saukaka Wa Masu Kananan Masana’antu Hanyar Samun Rance.’

An gudanar da taron ne a Gidan Gwamnatin Jihar Barno, da ke Maiduguri, inda Gwamna Babagana Zulum ya karbi bakuncin mahalarta taron, wanda shi ne irin sa na farko.

Ya ce an bayar da wannan lamuni ne ga mutane ko kananan da matsakaitan masana’antu  dubu 95 a jihohin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Okpanachi ya ce ko a bara sai da aka raba lamunin Naira biliyan 30 ga masu kananan masana’antu dubu 35. Ya ce wadanda aka ba lamunin, kashi 72 cikin 100 mata ne, yayin da kashi 51 cikin 100 kuma matasa ne.

An bayar da lamunin a karkashin kungiyoyin NACCIMA da SMEDAN da jami’o’i da sauran cibiyoyin hada-hadar kasuwanci.

Okpanachi ya ce akwai bukatar a rika bayar da lamunin domin inganta tattalin arziki, kasancewar akwai masu kananan masana’antu har miliyan 41.5 a kasar nan, wadanda da yawansu ba su samun damar karbar bashi daga bankunan kasuwanci.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya