✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bankin manoma ya raba wa manoma bashin Naira biliyan 150

Manajan Daraktan Bankin manoma na Najeriya [BOA] Alhaji Kabiru Adamu ya bayyana cewa bankin  ya raba wa manoma bashin Naira biliyan 150  cikin shekaru 40…

Manajan Daraktan Bankin manoma na Najeriya [BOA] Alhaji Kabiru Adamu ya bayyana cewa bankin  ya raba wa manoma bashin Naira biliyan 150  cikin shekaru 40 da kafuwarsa.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude rashen bankin a garin Lere dake Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna.

Ya ce an kafa bankin ne domin tallafawa manoma ta hanyar basu rancen kudade don bunkasa sana’ar noman da suke yi. Kuma  ana  bayar da rancen  ne ta hanyar kungiyoyin manoma.

Manajan Daraktan bankin, wanda wani babban jami’in bankin, Alhaji Muhammad Abdu Babangida ya wakilta, ya yi bayanin cewa sun bude reshen wannan banki a Karamar Hukuma Lere  ne, saboda kaurin  sunan da  yankin ya yi, wajen noma a Najeriya.

A nasa jawabin, mai martaba Sarkin Lere, Alhaji Garba Muhammad ya bayyana cewa babu shakka wannan banki zai dada karfafawa al’ummar karamar hukumar Lere gwuiwa  wajen bunkasa harkokin noma a  yankin.

Ya yi  kira ga  wadanda suka ci gajiyar samun rancen  su rika kokari suna biya, domin  bankin ya rayu.

Da yake jawabi manajan bankin manoman reshen Lere Muhammad Lawal Ahmed, ya yi bayanin cewa sun fara aiki ne, tun a watan Janairun da ya gabata.

Ya ce ganin irin noman da ake yi a yankin da wahalar da manoman  yankin suke  sha, wajen  zuwa wurare da rassan wannan banki yake, ya sanya suka yi ta rubuce rubuce, kan a kawo  bankin zuwa wannan yanki.

Ya ce wannan ne ya sanya hukumar bankin ta amince, aka zo aka bude wannan banki.

Ya ce a wannan rana sun baiwa mata guda 60 rance, wadanda suka fito daga kungiyoyi guda shida. Kuma rancen za a biya shi a cikin shekara daya.