✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barawon da ya saci kaya a coci zai sha daurin shekara 2 a gidan yari

Wata kotu mai daraja ta daya da ke zama a garin Karu, cikin Abuja ta yanke wa wani mai suna Sunday Ogoda, hukuncin daurin shekaru…

Wata kotu mai daraja ta daya da ke zama a garin Karu, cikin Abuja ta yanke wa wani mai suna Sunday Ogoda, hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda samunsa da laifin sace kaya a coci.

Wanda aka yanke wa hukuncin, mazaunin Kurudu, a Abuja ya amsa laifuffuka uku da ake tuhumarsa dashi a gaban kotun.

Mai shigar da kara Barista Adeyanju Ayotunde, ya fadawa kotun cewa wanda ake karan ya balle kuma ya shiga cocin Deeper Life da ke Kurudu, Abuja sau uku inda ya sace amsa kuwwa, talabijan guda biyar, fankar bango, da kuma tukunyar iskar gas mai nauyin kilogram 12 wanda jimillar kudinsu ya kai Naira dubu 386.

Ayotunde, ya kuma shaidawa kotun cewa wanda ake karar ya amsa laifuffukansa yayin da aka tuhume shi a ofishin ‘yan sanda.

Ya kuma bayyana cewa, an yi nasarar samo tukunyar iskar gas, talajiban guda biyu da kuma fankar bango, amma na’urar amsa kuwwar da kuma talabijan kirar plasma har yanzu ba a san inda suke ba.

An yanke wa wanda ake karar hukuncin ne bisa laifin ketarawa ba bisa ka’ida ba, balle gida da kuma sata wanda ya sabawa kundi na 348, 358 da 288 na hukunce-hukuncen doka.

Alkalin kotun, Ismail Abdullahi, ne ya yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan yari tare da tarar biyan Naira dubu 198 na kayayyakin da ba a dawo dasu ba.

A lokaci duga kuma, mai shigar da karar ya fadawa kotun cewa, tuni ’yan sanda suka kamo wadanda suka siya kayan satan.

Cikin wadanda aka kamo sun hada da: Yahaya Mohammed mai shekara 41, Kure Yahaya mai shekara 25, Khadijat Taiwo mai shekara 35 da kuma Mariam Emmanuel mai shekara 22, wadanda suka amsa laifin siyan kayan sata a gaban kotun, wanda laifin ya sabawa sashe na 317 na hukunce-hukuncen doka.

Alkalin kotun Ismail Abdullahi, ne ya yanke musu hukuncin wata 6 a gidan yari ko kuma kowannensu ya biya tarar Naira dudu 10.