Da Dumi Dumi

barayi sun kai hari gidan Aminu Hudu

A ranar Talatar makon jiya da misalin karfe 3:05 na dare ne barayi suka kai hari gidan Aminu Hudu wanda aka fi sani da Al-mah.
 Al-mah ya ce yana cikin barci barayin suka tayar da shi, daga nan suka ce ya ba su kudi, sai ya ce wallahi ba shi da kudi, sai wata yarinya a cikinsu ta ce idan ba shi da kudi zai sha duka, sai ta daga wani karfe za ta buga masa, sai wannan saurayi ya tare ta, ya ce ki bar shi ba ki gane shi ba ne? Sai yarinya ta ce wane ne shi? Sai saurayi ya ce dattijon arziki ne wanda yake fim din Hausa, su karbi rabonsu su tafi.
“A takaice dai sun kwace mana wayoyi hudu wadanda suka hada da Blackberry 1 da Nokia 2 da Samsung 1 da Naira dubu 5 da 170, da kuma sarkar gwal, daga nan sai suka kulle ni a bandaki har sai da suka fita sai maidakina ta zo ta bude ni.” Inji Al-mah.

Share