Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Barazanar ta’addanci ga harkar noma

A ranar Larabar makon jiya ce Ministan Harkokin Cikin gida AbdurRahaman Dambazau ya bayyana cewa ’yan ta’adda na barazana ga harkar noma a Jihar Zamfara wanda ya sanya ake tsoron hakan zai iya haifar da matsala a kokarin da ake yi na wadata kasa da abinci.

Babu shakka wannan tsokacin da Minista ya yi haka yake, domin kuwa ’yan ta’adda sun hana manoma sakat ba a Jihar Zamfara kawai ba har ma da wasu sassa na yankin Arewacin kasar nan, yankin da nan ne yake samar da dimbin abinci ga kasar nan.

ADVERTISEMENT

A Jihar Zamfara ’yan ta’adda sun hana manoma zuwa gonakinsu, idan kuma suka kuskura suka je to sai buzunsu. A wani lokacin kuma ’yan ta’addan sukan sanya wa manoman haraji ne su bukaci su biya kafin su kyale su su je gonakinsu, duk da haka kuma idan sun yi noman sai kwaso amfanin gonar ya zama matsala gare su.

Ba a Jihar Zamfara ba ne kawai manoma ke fuskantar matsala, a jihohi da dama na Arewacin kasar nan manoma na fuskantar barazana daga ’yan ta’adda inda kiri-kiri ’yan ta’addan suke hana mutane da dama  yin noma, wadanda kuma suka daure suka yi noman su kasa ci gaba da kula da gonar saboda tsoro.

ADVERTISEMENT

A lokuta da dama gonaki ’yan ta’adda suke zuwa suna yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, wani lokaci kuma a kan hanyar zuwa gona ko a kan hanyar komawa gida.

Akwai wani manomi da ya bayyana min cewa ya yi noma amma kafin amfanin ya isa girbi aka kira shi daga yankin da gonar tasa take aka ce masa kada ya sake zuwa gonar, yana ji yana gani ya hakura da gonar tasa bayan ya kashe makudan kudi.

Wani kuma yana dawowa daga gonar tasa aka kama shi aka yi garkuwa da shi sai da ya kwashe kwanaki a hannun wadanda suka yi garkuwa da shi suka sako shi bayan ya biya kudi, amma bai bayyana ko nawa ne ya biya  ba.

Yanzu kuma da amfani yake dawowa gida saboda kaka sai ’yan ta’addan suka koma suna kama manoman da suka yi noma da yawa inda dole a sayar da amfanin gonarsu a biya su kudin da suka bukata kafin su sake su.

Mutane da dama masu karamin karfi da noma ne suke takama ko da kuwa suna da wata sana’a da suke yi, kamar kanana da matsakaitan ma’aikata da masu sana’o’in hannu da dama, duk wadannan suna hada aikinsu da noma ne domin samun saukin rayuwa, domin idan ba su yi noman ba abin da suke samu ba zai iya rike su tare da iyalinsu ba.

Saboda haka yanzu an tsorata manoma, masu dukiya kuma da suke sha’awar shiga harkar noma su ma sun tsorata, domin suna jin tsoron zuwa gona saboda kada masu garkuwa su kama su.

Noma da kiwo su ne manyan abubuwan da yankin Arewa yake takama da su, amma yanzu an himmatu wajen kassara su. Da can a baya rikicin makiyaya da manoma ake fama da shi a yankin. Sai aka koma satar shanu gadan-gadan wadda ta sanya harkar kiwon dabbobi ta zama matsala, masu kudi suka rika dari-dari da harkar. Yanzu kuma ga shi an sanya harkar noma a gaba ana so sai an gurgunta harkar.

Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo yana yawan shawartar al’ummarsa da su yi karatu, su yi noma, su yi kiwo. Yanzu duk wadannan muhimman abubuwan guda uku suna fuskantar barazana a yankin Arewa.

Ya kamata masu kokarin gurgunta harkokin noma da kiwo su fahimci cewa sai da abinci ne za su iya zama lafiya har su yi walwala, komai yawan kudin da suka tara idan akwai karancin abinci ba za su ji dadin kudin ba, domin abinci shi ne gaba da komai, Hausawa suna cewa, ‘sai da ruwan ciki ake jan na rijiya.’

Muna rokon Allah Ya tausasa zukatan masu wannan mugun nufin su daina, kuma su fahimci cewa’ mugunta fitsarin fako ne.’ Ita kuma gwamnati wajibi ne ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin mutanenta domin shi ne babban aikinta. Su kuma sauran jama’ar kasa su ci gaba da yin addu’a domin Allah Ya kawo karshen wannan matsala.

Ba don wadannan ’yan ta’addan ba da a halin yanzu abinci ya wadata kuma farashinsa ya sauko sosai, saboda mutane da yawa suna da sha’awar yin noma amma rashin kwanciyar hankali a gonaki ya sanya suna dari-dari da harkar.