✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona da Neymar za su ci gaba da sa-in-sa a kotu

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun ce a ranar 27 ga Satumba ne za a ci gaba da sauraron kararrakin da FC Barcelona da…

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun ce a ranar 27 ga Satumba ne za a ci gaba da sauraron kararrakin da FC Barcelona da Neymar suka kai kotu, inda kowane bangare ya dage shi ne mai gaskiya.

Kafar labaran wasanni ta as.com, ta ce a ranar ce za a ci gaba da sauraron karar da aka sha dagawa.

Da farko an shirya za a ci gaba da sauraron karar ce a ranar 31 ga Janairun bana, amma aka rage kwanaki biyu zuwa ranar 28 ga Janairun bana.  Daga nan aka sake dagawa zuwa ranar 21 ga  Maris, sannan aka sake dagawa zuwa 27 ga watan Satumban nan.

Barcelona ta kai karar Neymar ne a kan ya mayar mata Yuro miliyan 14 (kimanin Naira biliyan 55 da miliyan 300) a matsayin kudin kwantaragin da suka kulla da dan kwallon a lokacin da ya canja sheka zuwa kulob din amma bai kammala kwantaragin ba sai ya koma kulob din PSG  yayin da Neymar kuma yake karar Barcelona ta cika masa Yuro miliyan 26 (kimanin Naira biliyan 107 da miliyan 70)  su zama Yuro miliyan 40 a matsayin cikon kudinsa na kwantaragin da ya kulla da kulob din kafin ya canja sheka zuwa kulob din PSG na Faransa.

Barcelona ta ce duk da sun kulla yarjejeniya da Neymar a kan za ta cika masa Yuro miliyan 40  amma kafin wa’adin ya cika sai ya sake canja sheka zuwa PSG na Faransa a kan Yuro miliyan 222 (kimanin Naira biliyan 876 da miliyan 90) wanda hakan ya sa sawun giwa ya take na rakumi don haka Neymar ne yak amata ya mayar wa Barcelona Yuro miliyan 14 da ta ba shi tunda farko amma dan kwallon ya ce atafau sai kulob din ya cika masa ragowar Yuro miliyan 26 da suka yi yarjejeniya tun farko.

Yanzu dai an zuba ido ne a ga yadda wannan shari’a za ta kaya a wata kotu da ke kasar Sifen.

Duk da wannan shari’a da ke tsakaninsu, bai hana kulob din FC Barcelona sake zawarcin Neymar don ya koma can ba.  Sai dai kawo yanzu hakan bai yiwu ba saboda wasu dalilai.