Search
Subscribe
Barcelona ka iya sayen dan wasa duk da an rufe kasuwar

Suarez da Dambele

Barcelona ka iya sayen dan wasa duk da an rufe kasuwar

Jinya mai tsawo da Ousmane Dembele da Luis Suarez za su yi ce ta tsunduma Barcelona cikin neman dan wasan gaba duk da cewa, an rufe kasuwar saye da musayar ‘yan wasa a Nahiyar Turai.

Ko ta yaya hakan zai yi wu?

Luis Suarez, ba zai dawo fili ba sai ya yi jinyar wata hudu sakamakon rauni a gwiwarsa, yayin da shi kuma Dembele zai shafe wata shida saboda rauni a bayan gwiwarsa.

A karkashin tanadin dokar gasar La Liga ta Sifaniya, idan dan kwallo ya ji raunin da zai kai shi ga jinyar wata shida to kungiyarsa za ta iya neman a ba ta damar sayen dan wasa daga kungiyar La Liga ko kuma dan wasan da ba shi da kulob a Sifaniya.

Barcelona wadda ke ta biyu a teburin La Liga, ta aika da rahoton halin da Dembele yake ciki ga hukumar La Liga, wadda za ta duba ta ga ko Barca ta cancanci a ba ta damar ko kuma a’a.

Sai dai babu tabbas ko hukumar za ta bai wa Barca wannnan dama, kamar yadda wani kwararre kan gasar La Liga, Gullem Balgue, ya shaida wa BBC Radio 5 live.

Ya ce: “Kwararru masu zaman kansu kan harkar lafiya ne ke duba rahotannin jinya da ‘yan wasa za su yi kuma babu tabbas ko za su yarda cewa jinyar Dembele za ta kai wata shida. Saboda jinyar da ya yi daga irin wannan rauni a baya wata uku da rabi ya yi.

“Wata hanya ce ta zabin gaggawa ga duk kulob din da hakan ta faru da shi kuma kungiyoyin ne suka sahale ta da kansu.”

Daga cikin wadanda Barca ke neman dauka sun hada da: Lucas Perez na kungiyar Alaves, wanda ya ci kwallo tara a wasa 22 a kakar bana. Sai kuma dan Getafe, Angel Rodriguez mai shekara 32, da kuma Willin Jose na Real Sociedad, wanda ya kusa komawa Tottenham a watan Janairu.

Idan aka bai wa Barca damar, za ta kara karfi yayin da su kuma abokan hamayyarta ba su da wannan ikon.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin