Da Dumi Dumi

Barca ta rage farashin Umtiti; zuwan Haaland Madrid sai 2022, wa Arsenal ke nema?

Samule Umtiti
Samule Umtiti (Hoto: Diario AS)

Shirye-shirye sun yi nisa a Camp Nou na kokarin dauko Lautaro Martinez wanda hakan ya sa kungiyar Barcelona ta sassauta farashin Umtiti saboda ta samu kudin biyan albashi idan ta kawo Martinez din.

A gefe guda, dole ne kungiyoyin Real Madrid da Manchester United su hadiye aniyarsu ta dauko Haaland har zuwa shekarar 2022 saboda hukumomi a Dortmund ba su da burin sakin dan wasan.

Ita kuwa Arsenal kokari ta ke yi na sayen ‘yan wasa daga kungiyoyi daban-daban. Ko su wane ne?

Barcelona ta rage farashin Umtiti

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sauke farashin dan wasan bayanta Samuel Umtiti zuwa Euro million 30.

ADVERTISEMENT

Kokarin da take yi na kulla yarjejeniya da dan wasan Inter Milan, Lautaro Martinez, ya sa kungiyar ta yankin Kataloniya tana fadada hanyoyin tattara kudade saboda biyan albashin dan wasan idan ya sanya hannu a kan kwantiragin da ta mika masa.

Jaridar Sport ES ta rawaito cewa a shirye kungiyar ta Barcelona take ta mika Umtiti wanda dan kasar Faransa ne saboda rage yawan kudin da za ta biya don dauko Martinez.

Duk da cewa dan wasan mai shekara 26 yana fama da jinya, kungiyar tana sa ran za a amince da bukatar ta sayar da shi idan ya warke.

Zawarcin Haaland da Madrid take yi zai kai 2022

Wata jaridar wasanni da ke kasar Ingila, Standard Sport, ta rawaito cewa zawarcin da kungiyoyin Real Madrid da Manchester United suke yi na ganin sun dauko sabon dan wasan kungiyar Borussia Dortmund Erling Haaland zai kai su shekarar 2022.

Jaridar ta bayyana cewa hakan zai kasance ne saboda yadda sabon dan wasan yake haskawa da kuma burge hukumomi a kungiyar ta kasar Jamus.

Dortmund ta dauko matashin dan wasan ne a kan Euro miliyan 23 a watan Janairu wanda tuni shugaban kungiyar Real Madrid Fiorentina Perez da hukumomi a Old Trafford suka nuna sha’awar dauko shi.

Sai dai burinsu na dauko dan wasan ba zai yi nasara ba saboda a halin yanzu yana da kwantiragi a kungiyar da zai kai shi zuwa shekarar 2020.

A kwantiragin nashi dai farashin dan wasan ya kai Euro miliyan 75 a halin yanzu.

Tattaunawa za ta ci gaba tsakanin Arsenal da Akanji

Tattaunawa a kan bukatar da kungiyar Arsenal ta gabatar ta dauko dan wasan Dortmund, Manuel Akanji, tun a watan Janairu za ta ci gaba, bayan da kungiyar ta sabunta bukatar ta da Euro miliyan 25.

Arsenal din dai ta fara zawarcin dan wasan tun kakar bara wanda bai samu nasara ba saboda sayar da dan wasan ta Abdou Diallo da ta yi wa kungiyar PSG.

Dawowar da aka yi da wasannin Bundesliga ya sa kungiyar ta sake mai da hankali wurin kokarin dauko dan kasar Switzerland din mai shekara 24.

Shirye-shiryen sauya sheka

Sauran shirye-shiryen sauya sheka da ‘yan wasa ke yi sun hada da:

Shirin da Arsenal ta ke yi na dauko Adrien Rabiot saboda ta karfafa ‘yan wasan tsakiyar ta.

Liverpool ta daura damarar sayo dan wasan baya na Sevilla Diego Carlos.

PSG ta na sha’awar dauko Aubameyang duk da ragowar shekara daya a kwantiraginsa a Arsenal.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya