✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta sa Dembele a kasuwa

Kulob din FC Barcelona na Sifen ya sanya dan kwallonsa Ousmane Dembele a kasuwa.  Kamar yadda jaridar Don Balon ta Sifen ta kalato a shekaranjiya…

Kulob din FC Barcelona na Sifen ya sanya dan kwallonsa Ousmane Dembele a kasuwa.  Kamar yadda jaridar Don Balon ta Sifen ta kalato a shekaranjiya Laraba, an nuna kulob din ya sanya farashin Yuro miliyan 110 kimanin Fam miliyan 95 (kimanin Naira biliyan 44 da miliyan 745) ga duk kulob din da ke bukatarsa.

Mahukuntan kulob din ne suka yanke shawarar sayar da dan kwallon ganin yadda ake yawan samun sabani da shi.

Rahotanni sun nuna kulob din Bayern Munich da ke Jamus da Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa sun nuna sha’awarsu a kan Dembele dan shekara 21 da haihuwa.