Da Dumi Dumi

Barcelona ta sallami kocinta ta maye gurbinsa da tsohon kocin Real Betis Quique Setien

Barcelona ta sallami kocinta Ernesto Valverde tare da maye gurbinsa da tsohon kocin Real Betis Quique Setien.

Valverde, mai shekara 55, ya taimakawa Barcelona lashe kocin La Liga biyu a jere, kuma shi ke saman tebur da yawan kwallaye a bana.

Sai dai Barcelona ta fuskanci koma baya karkashinsa inda ta kasa lashe kofin zakarun Turai.

Setien, mai shekara 61, ya taimakawa Betis zuwa matsayi na shida a teburin La liga a 2005 da kuma zuwa wasan dab da karshe a Copa del Rey kafin ajiye aikinsa a watan Mayu, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Ya amince da yarjejeniyar shekaru biyu da rabi kuma a gobe Talata ne Barcelona za ta gabatar da shi ga ‘yan jarida.

ADVERTISEMENT

A cikin sanarwar da ta fitar, Barcelona ta ce Valverde ya amince ya kawo karshen aikinsa tare da gode masa kan kwarewarsa da kuma jajircewarsa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya