✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta yi sabon koci

A ranar Litinin da ta gabata ce ne kulob din FC Barcelona da ke Spain ya kori tsohon kocinsa inda nan take ya maye gurbinsa…

A ranar Litinin da ta gabata ce ne kulob din FC Barcelona da ke Spain ya kori tsohon kocinsa inda nan take ya maye gurbinsa da wani.  Sabon Kocin shi ne Kuikue Setien toshon Kocin kulob din Real Betis da ke Spain.

Kulob din ya ce ya dauki wannan mataki ne ganin yadda kulob din yake tangal-tangal a kaka ta bana.  Na baya-bayan nan shi ne yadda kulob din Atletico Madrid ya lallasa Barcelona da ci 3-2 a gasar cin Kofin Royal Super Cup da aka yi a Saudiyya.

Rahoton da kafar watsa labarai ta UK Edpress da ke Ingila ta kalato, ya ce Barcelona ta kori tsohon kocinta Ernesto Balberde mai shekara 55 ne ganin yadda kulob din AS Roma na Italiya da na Liberpool da ke Ingila suka doke Barcelona a matakin kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai a shekarar 2018 da kuma a 2019.

Sabon kocin Kuikue Setien mai shekara 65 bai da tarihi wajen lashe wani kofi a Spain a lokacin da ya horar da kulob din Betis sannan ya kulla yarjejeniya da Barcelona ne zuwa ranar 30 ga watan Yunin bana.