✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona tana zawarcindan kwallon Najeriya Chukwueze

  Rahotannin da ke fitowa daga kulob din FC Barcelona na Sifen sun nuna kulob din ya fara zawarcin dan kwallon Billareal kuma dan asalin…

 

Rahotannin da ke fitowa daga kulob din FC Barcelona na Sifen sun nuna kulob din ya fara zawarcin dan kwallon Billareal kuma dan asalin Najeriya Samuel Chukwueze.

Alamu sun nuna kulob din yana son rabuwa da dan kwallonsa Philippe Coutinho ne don maye gurbinsa da Samuel Chukwueze.

A kakar bana, kwallaye 7 kacal Coutinho ya zura a raga a dukkan wasannin da ya yi wa FC Barcelona.

A bana, Samuel ya haskaka a gasar La-Liga ta Sifen a kulob din Billareal da hakan ta sa kungiyoyi da dama suke zawarcinsa ciki har da na FC Barcelona.

Samuel Chukwueze na daga cikin ’yan kwallon da ake sa ran za su yi wa Super Eagles wasa a gasar cin kofin Afirka da za a yi a kasar Masar a wata mai zuwa.