✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barebari na shirin danne mu – Sultan Jibrin

Sarkin Shuwa-Arab na Jihar Legas Sultan Jibrin Yahya, ya koka kan abin da ya yi zargi da danniyya da al’ummar Barebare suke yi wa Shuwa-Arab…

Sarkin Shuwa-Arab na Jihar Legas Sultan Jibrin Yahya, ya koka kan abin da ya yi zargi da danniyya da al’ummar Barebare suke yi wa Shuwa-Arab da sauran kananan kabilun Jihar Barno inda ya ce ba a jihar ta Barno kadai ba, hatta su ma da suke Kurmi lamarin na shafarsu.

Sarkin Shuwa-Arab din ya shaida wa Aminiya hakan ne a fadarsa da ke Oluti a yankin Festac a Legas inda ya ce an nada shi a Sarkin Shuwa-Arab na Jihar Legas tun a 1991. Ya ce sarautar Shuwa -Arab a Jihar Legas ta samo asali ne lokacin da Janar Mamman Shuwa da Sufeto Janar Alhaji Kam Salim suka jagoranci kafa sarautar Shuwa-Arab a Legas saboda a wanccan lokaci al’ummar Shuwa ba su da masarautar gargajiya da ta hade kansu sai dai kungiya/ Ya ce sai suka ga lokaci ya yi da ya kamata a nada Sarkin Shuwa-Arab sai aka nada Sarki na farko Alhaji Shehu Wanu wanda daga baya ya koma Arewa da zama. Ya ce lokacin da Asheikh Jarma yake Minista a gwamnatin Shehu Shagari ne sai ya zo suka nada wani sabon Sarkin Shuwa-Arab Sarki Fubu. “Daga nan rashin ilimi da tsari ya yi wa tsarin sarautar tarnaki aka sake mai da ita kamar kulob sai muka hadu tare da kungiyarmu ta Alhaya masu sana’ar dabobbi don a yi gyara inda a karshe aka zabe ni na zama Sarkin Shuwa Arab. Tun ba na so mutane suka ce sai ni, a haka na yarda na karba. Sannan SarkIn Legas wato Oba na wancan lokacin ya sanya hannu har ya ba ni takardar shaida a matsayin Sarkin Shuwa Arab na Jihar Legas. Kuma idan na je gida Jihar Barno ina zuwa Fadar Shehun Borno in kai gaisuwa wajensa domin neman tubararki da goyon baya. Na je wajen Shehun Barno kimanin shekara 15 sai ya rubuta min takardar shaida amma sai ya ce dole in zamo a karkashin Mai Kanuri na Legas wato Sarkin Barebari Mustafa. In zamanto ina karkashinsa ina yi masa biyayya bayan sarautata ta riga tasa kuma shi ba ya jin harshenmu.Yaya za a yi ni da jama’ata mu koma karkashinsa?”

Sultan Jibrin Yahya ya ce, “A haka na dawo muka hakura ni da jama’ata muka tattauna cewa za mu ci gaba da biyayya ga Shehun Borno amma mu ba zam u lamunci kasancewa a karkashin Mai Kanuri na Legas ba, domin sarautarmu ta riga tasa muna kuma da ’yanci da walwalar tsayawa da kafarmu ba tare da wani ya bautar da mu ko ya yi mana danniya ba.”

Ya ce a ’yan watannin da suka shude Mai martaba Shehun Borno ya ba da umarnin cewa, an tube shi domin ba ya zuwa fadar Mai Kanuri na Jihar Legas, “Don haka ni da jama’ata muka ce hakan ba za ta sabu ba, ba zai yiwu a yi mana karfa-karfa ko danniya da murdiya ba, domin mu ma muna da ’yancin mu jagoranci al’ummarmu ba sai mun zauna a karkashin Barebari ba. Suna yi mana barazana da sojoji da ’yan sanda. Wannan barazana ba za ta yi tasiri ba, domin akwai doka da oda a wannan kasa sannan akwai hukuma kuma akwai kotu, za mu bi duk hanyoyin da suka dace domin bibiyar hakkinmu,” inji shi.

Ya kara da cewa, suna ci gaba da biyayya ga Mai martaba Shehun Borno amma suna rokonsa ya guji abin da zai kawo rikici ko rarrabuwar kai a tsakanin al’ummar Shuwa-Arab da Barebari mazauna Jihar Legas.