Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Barebari sun fi Fulani kamuwa da COVID-19

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule

Barebari sun fi Fulani kamuwa da COVID-19

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce duk da cewa shi Babarbare ne, ya damu da yadda cutar coronavirus ke ci gaba da kama mutane a Lafiyar Barebari, babban birnin jihar.

‘Ya fadi haka ne a Gidan Gwamnati da ke Lafiya, yayin taron majalisar jiha na mako-mako inda ya nuna damuwa da yadda birnin na Lafiyar Barebari ya yi wa Karamar Hukumar Keffi, garin Fulani zarra wajen yaduwar cutar.

A cikin mako guda, birnin Lafiya ya samu mutum 35 da suka kamu da cutar sai Karu da mutum 78 sannan a Keffi 31.

Gwamnan ya ce rashin kiyayewa daga mutanen Lafiya ke jawo hauhawar cutar, domin suna karya dokar da gwamnati ta gindaya don rage kamuwa da annobar.

Ya ce, “Karu ita ce kan gaba, kuma ta zama kalubale, don a mako guda an samu masu dauke da cutar har 78 a gwaji 193 da aka gudanar, sannan Keffi ta samu 31.

“Abin damuwa shi ne yadda garin Lafiya ya yi wa Keffi zarra.”

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda wadansu mazauna birnin Lafiya ke yi wa doka karan-tsaye, duk da kasancewarsa fadar Jihar Nasarawa.

Don haka ya yi kira ga mambobin Kwamitin Yaki da cutar COVID-19 su dage wajen wayar da kai domin mutanen Lafiya su rika kiyayewa.