Da Dumi Dumi

Barka da sabuwar shekara

Tartsatsin wuta mai ban sha’awa ya kawata sararin samaniya a wasu sassan duniya – shekaranjiya – Laraba 1 ga watan Janairun nan – domin murnar shigowar sabuwar shekarar 2020 Milidiyya – a tsarin kalandar Gregory ta Rumawa. A nan Najeriya ana maraba da sabuwar shekarar a matsayin ranar hutu kuma tana nuna an bude sabon babi ta fuskar sabuwar alkibla tare da fara aiki da sabon kasafin kudin kasar nan.

Sabuwar shekarar za ta zama dan ba wajen nuna juriyar ’yan Najeriya, yayin da muke cike da fatar tattalin arzikinmu ya inganta. Sai dai a daidai wannan gabar, ma’aunan mizanin arzikinmu ba sa kan yanayin da muke son ganinsu. Mizanin hauhawar farashi a Najeriya ya kai kashi 11.85 a watan Nuwamban bara. Wanda hakan ya zama mafi muni tun watan Afrilun 2018 daga kashi 11.61 a watan da ya gabata. An yi kiyasin cewa matsalar rashin  aiki za ta kai kashi 33.5 a wannan shekara. Matsalar wutar lantarki ita ma za ta ci gaba da ta’azzara; yayin da hanyoyin sufuri da sauran ababen more rayuwa su ma suke cikin mummunan yanayi. ’Yan Najeriya dai na cike da fata tare da addu’ar Allah Ya kawo hanyoyin da za su sa a yi adabo da tarin matsalolin a wannan Sabuwar Shekara.

Wani bangaren da ’yan Najeriya ke zumudin samun sa’ida cikin gaggawa shi ne batun cin hanci, wanda har yanzu yake ci gaba da cin dunduniyar kasar. Gwamnati dai ta sha babatu sau shurin masaki kan batun. Sai dai wannan batu ba abu ne da kawai za a yi ta yaki da shi ba: a’a kamata ya yi a ga hakan a dabi’u da halayyar dukkan jami’an gwamnati a kowane mataki. Cin hanci ya gurbata dukkan sassan rayuwar al’umma; sannan ya hana ’yan Najeriya damar samun ingantacciyar rayuwa. Ya kamata a yaki wannan muguwar dabi’ar ta sabbin hanyoyin fasaha tare da hanyoyin dauri da aka saba da su na shugabanci abin koyi.

Batun yaki da cin hanci dai ba aiki ne da ya rataya a wuyan mutum guda ba; don haka muna kyautata zaton Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci ’ya’yan jam’iyyarsa tare da gwamnatinsa wajen jan ragamar yakar rashawa. A halin yanzu dai, akwai gagarumin bambanci a tsakanin furuci da aiki a zahiri daga jiga-jigan gwamnati. Ya kamata mu duba batun fiye da batun kambama al’amarin bankadowa da kwato wasu kudade da Hukumar EFCC da takwarorinta ke ta ikirarin yi. Kari kan manyan bincike da shari’o’i da hukunce-hukuncen da take samu, kamata ya yi a ce an yi wa tufkar hanci wajen hana rashawar – ba wai kawai a dogara da ladabtar da masu zarmiyar ba.

A daidai goshin karewar shekarar 2019, an samu yawaitar hare-haren Boko Haram da Kungiyar ISWAP. Garkuwa da jama’a da aikace-aikacen ’yan bindiga tare da wasu miyagun laifuffuka har yanzu suna ci gaba da illata rayuwar dan Adam a wasu sassan kasar nan da dama. Bangaren tsaro guda wanda za a iya bugun kirjin samun sa’idarsa, shi ne na raguwar samun tada zaune-tsaye tsakanin manoma da makiyaya. Ayyukan ’yan bindiga da kashe-kashen babu gaira babu dalili su ma sun dan sarara a Jihar Zamfara; sakamakon tsauraran matakan da gwamnatin jihar tare da jami’an tsaro suka dauka.

ADVERTISEMENT

A wannan Sabuwar Shekarar dai, muna sa ran sojoji da hadin gwiwar jami’an tsaro da na Sibiliyan JTF su dauki kwararan matakan tsaro da za su kawo karshen duk wata barazanar tsaro a sassa da dama na kasar nan. Ita kuma Gwamnatin Tarayya, wajibi ne a kanta ta sake lale kuma ta zage dantse ta kara samar da kayayyakin yaki tare da mara baya ga makwabtanmu wajen ganin karshen barazanar da kungiyar Boko Haram take yi a kasar nan dungurungum. Ya kamata ’yan Najeriya su yaba da irin azama da himmar aikin da sojoji da sauran jami’an tsaron kasar nan ke nunawa; wadanda a halin yanzu ma za a iya cewa ayyukan wanzar da lumana ya sha musu kai nesa ba kusa ba: Sai dai duk da haka suna bakin kokari wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.

Dukkan ’yan Najeriya sun hadu wajen murnar amincewa da dokar kasafin kudin Gwamnatin Tarayya a kan kari – domin kawai a dawo kan turbar nan ta tsarin kasafin kudi na daga watan Janairu zuwa Disamba. Kodayake, wannan somin tabi ne kawai. Muna sa ran ganin sakamako mai ma’ana a wannan shekara, ta hanyar samar da kudade cikin hanzari kuma isassu tare da kare ayyukan raya kasa da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da yakar fatara a kasar nan, cikin kankanen lokaci.  

Sabuwar Shekarar ta bude kofar dama ga Najeriya wajen tunkarar kalubalen da suka yi mata dabaibayi – wala’alla ko ’yan kasar za su dara tare da samun yalwar arziki a shekarar. Kuma ita ce shekarar da ya kamata ’yan Najeriya su yi watsi da bambance-bambancen siyasa tsakaninsu – domin zama cikin aminci da juna. Yayin da aka koma bakin aiki jiya Alhamis, ya kamata a ce an samu sabon yunkuri na nuna jajircewa musamman daga dukkan ma’aikata domin kara inganta yanayin aiki wajen bayar da gudumawarsu ta fuskar zaburar da ci gaban kasa.

Muna yi wa dukkan ’yan Najeriya barka da kuma fatar samun yawataccen aminci a Sabuwar Shekarar.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya