Da Dumi Dumi

Barka da Sabuwar Shekarar 2019

Ranar Talatar da ta gabata 1 ga Janairu ce ta kasance rana ta farko ta Sabuwar Shekarar 2019. Daga dukan alamu shekara ce da take cike da dimbin alkawura, kuma fatarmu da addu’armu wannan shekara ta kasance mai dimbin alheri ga rayuwarmu da kasarmu da jama’armu da kuma al’ummar Afirka da na sauran duniya.

Ga Najeriya, 2019 shekara ce ta zabe da take zuwa da dimbin abubuwan farin ciki kuma take cike da fargabar abin da ba a sani ba. Kamfe din zabe ya kankama kusan wata biyu da suka gabata, kuma gaskiyar magana ’yan tashe-tashen hankula da suka rika faruwa a wannan lokaci kadan ne idan aka kwatanta da baya.  Wannan abu ne mai karfafa gwiwa da ya kamata ya dore.

A sakon Sabuwar Shekara na Shugaba Muhammadu Buhari a safiyar ranar ya ce kada a rika daukar zabe a matsayin abu na ko-a-mutu-ko-a-yi-rai. Kuma ya yi alkawarin tabbatar da zaman lafiya a kasar nan lokacin gudanar da zaben. Wannan babban abin farin ciki ne. Bai kamata a rasa wata gaba ko rai ta mutanen kasar nan ba saboda kamfe ko zabe. Don haka wajibi ne a kan dukan hukumomin tsaro da jam’iyyu da mutanen da lamarin ya shafa su tashe tsaye wajen tabbatar da cewa zabe mai zuwa ya gudana cikin lumana kuma cikin gaskiya da amana. Bana ce shekara ta 20 da dawowar mulkin dimokuradiyya a kasar nan. Yana da muhimmanci a kanmu mu nuna wa kanmu da kasashen duniya cewa dimokuradiyya ta kafu a Najeriya. Lokaci ya yi da za mu yi watsi da miyagun abubuwan da suka zama ado a siyasar kasar nan a shekara 20 da suka gabata. Daya daga cikinsu ita ce ta sayen kuri’u, kuma muna fata Hukumar INEC da hukumomin tsaro za su dauki matakan da za su rage wannan muguwar dabi’a.

Babbar matsala ta biyu ita ce wadda ta shafi harkokin tattalin arzikinmu. A shekarar 2018 ne kasar nan ta fice daga masassarar tattalin arziki kuma har yanzu ba ta gama murmurewa daga illarta ba. Kuma a wani mataki na kawar da radadin masassarar tattalin arzikin ce gwamnati ta tsara shirin Farfado da Tattalin Arziki da Bunkasa shi (ERGP). Bisa lura da shirin ERGP, kasafin kudin bana da Shugaban Kasa ya mika ga Majalisar Dokoki ta Kasa a kwanakin baya ya tanadi yadda za a fadada shi. Kasafin bana ya yi jinkiri saboda Shugaban Kasar ya mika shi ne a watan Disamba. Damuwarmu ita ce idan Majalisar Dokoki ta Kasa ta tafiyar da shi irin yadda ta saba a shekarun baya da kuma lura da cewa lokacin kamfe zai mamaye watanni hudu na farkon bana, to za mu iya sake haduwa da mugun jinkiri. Wannan ba zai haifar da da mai ido ba wajen hanzarta farfado da tattalin arzikin.

Wani muhimmin bangare na harkokin rayuwar kasarmu a daidai lokacin da muka shiga Sabuwar Shekara shi ne rashin tsaro. A daidai lokacin da shekarar bara ta kare an samu mummunar farfadowar hare-haren mayakan Boko Haram a Arewacin Jihar Borno. Akalla muhimman garuruwa shida masu mutane da yawa maharan suka kwace a Karamar Hukumar Kukawa. Muna da yakinin cewa sojoji da hadin gwirar Sibiliyan JTF da sauran hukumomin tsaro za su hanzarta kwato garuruwan da aka kwace. Kuma muna sa ran su sake dabara da sake fasali da samar da makamai, kuma tare da taimakon makwabtanmu don kawo karshen ta’addancin Boko Haram kowa ya huta.

ADVERTISEMENT

Kuma halin da ake ciki a Jihar Zamfara abu ne mai daga hankali sosai, a daidai lokacin da shekarar bara ta kare mun riga mun yi kiran a kafa dokar ta-baci a jihar. Mun lura cewa sojoji da sauran hukumomin tsaro suna shan wahala, amma kasa tana da hakki a kansu na su hanzarta dawo da zaman lafiya a Jihar Zamfara da sauran wuraren da ake fama da tashin hankali a sassan kasar nan.

Muna taya daukacin ’yan Najeriya murna, zaman lafiya da kyakkyawar rayuwa a Sabuwar Shekara.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya