✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barkanmu da Sabuwar Shekara

Dukan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya raya mu muka ga wannan sabuwar shekara. Duk da cewa na lura a kan manta da irin…

Dukan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya raya mu muka ga wannan sabuwar shekara. Duk da cewa na lura a kan manta da irin wadannan tunatarwa idan shekarar Musulunci ta zo, to amma abin yi shi ne a rika tunatar da juna kuma a rika dora wasu al’amurra na gwamnatin da ta samu dama a kan kalandar Musulunci.

Lissafin rayuwarmu a yau da yawa tana da alaka da wannan kalandar, Musulmi ko waninsa. Misali shekarar haihuwa da shekarar shiga makaranta da shekarar kama aiki da shekarar samun ci gaba a aiki da shekarar kammala aiki da albashi na wata-wata da dai sauransu. Amma duk da haka mun san matsayin shekarar kuma ba ta yi tasiri a akidarmu ba, Alhamdulillah.

Salati da taslimi ga Shugabanmu dan gatan Allah, wanda duniya ba ta samu kamarsa ba, wanda ya yi bushara da Aljanna ga masu kyakkyawan aiki kuma ya yi gargadi da wuta ga masu munanan ayyuka.

Hakika shekarar da ta gabata ta zo da abubuwa na farin ciki da na bakin ciki kamar yadda aka saba. Aya ta tabbatar mana cewa duk abin da ya same ku daga sakamakon ayyukanku ne kuma a hakan ma Allah Yana afuwa da yawa a kan abin da muke aikatawa. Allah Ya yi mana afuwa.

A cikin al’umma, wani ya rasa muhallinsa, wani ya rasa matarsa, wani ya rasa iyayensa wani ya rasa jarinsa. A lokaci guda kuma wani ya samu alherin da bai taba samu ba a rayuwa da dai sauransu.

Duk wadannan abubuwa sun faru sai dai tarihinsu ko tasirinsu. A gwamnatance an kaddara za a yi ayyuka da cimma kudirori iri-iri, wasu an cimma, wasu kuma babu labarinsu. Amma abin lura a nan shi ne wane darasi muka dauka a kan abin da ya shude domin inganta abin da zai zo? Wannan tunatarwa a kansa take magana amma a takaice.

  1. a) Rayuwa da ma’anoninta: Rayuwa dai ba wata a ba ce ba illa wani jin dadi da Allah Ya hore wa dan Adam domin dan Adam ya gode maSa ta hanyar bauta maSa. Kamar yadda Allah Ya ce “Ba Mu halicci mutum da aljani ba face don su bauta Mini.” A wata ayar kuma Ya ce “Shi ne wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku a kan wanda ya fi ku kyautata aiki.” (Mulk, 2). Saboda haka a kowace gaba zai iya daukar rai ko Ya kawo wata. Wannan ya nuna mu zama cikin shirin ko-ta -kwana. Ina ganin a wannan lokacin abubuwan da suke bayyana na kudirar Allah suna da yawa. Misali ko makon shekaranjiya an samu wata rasuwa ta wata matashiya wadda ake shirin daurin aurenta domin a kai ta dakinta, ashe shirin kai ta makabarta ake yi. Allahu Akbar! Idan ko haka ne, wajibi ne mu yi biyayya ga fadin Allah Tabaraka Wa Ta’ala cewa “Duk wanda yake fatan haduwa da Ubangijinsa to ya yi aiki na kwarai kuma kada ya hada wani da Ubangijinsa a wajen bauta.” (Kahf, 110). Bahaushe ya ce kowag gyara ya sani kuma kowab bata ya sani. Allah Ka ba mu ikon gyarawa. Wanda kuma ya zabi batawa ko don jin dadi na dan lokaci sai ya tanadi masu kare shi idan azaba ta taho ko a duniya ko ranar gobe Kiyama idan yana da su. Allah Ka tsare mu.
  2. b) Jagorancin al’umma: Wannan gaba ce mai muhimmanci domin kuwa zaman al’umma babu jagoranci ko da na sa’a daya ne za a iya samun mummunar barna ko daga ciki ko daga waje. Al’ummar Musulmi a Najeriya ta samu nakasu a wajen jagoranci domin kuwa yanzu babu wani shugaba da zai ba da umarni ko hani a yi masa biyayya baki daya. Sauran shugabanni na kabila wadansu suna samun nasara a wajen wannan bangare kuma wannan hadin kan yana kawo musu ci gaba. Saboda haka wajibi ne shugabanni su ci gaba da nemo mafita game da hadin kan Musulmi a kasa. Sarkin Musulmi yana kokarinsa amma ka ga ba shi da wuka da nama. To da shugabanni Musulmi masu mulki a hannu za su mai da hankali sai su cike wannan wakeken gibi.
  3. c) Manyan matsaloli da ake fama da su: Tsaro, talauci, rushewar tarbiyya.

Babu shakka shekarar da ta gabata ta zo da abubuwa marasa dadi a harkar tsaro a Najeriya. Wannan ya hada da matsalar Boko Haram da ta ki ci, ta ki cinyewa a Maiduguri da Yobe da matsalar tsaro a Zamfara wadda take sabon shafi ne da ba a san shi ba a baya da matsalar masu garkuwa da mutane da rikicin Kaduna da na makiyaya da Fulani a sauran wurare. Idan ka dauki irin su Zamfara da aka sani da zaman lafiya, amma yau an wayi gari al’umma suna kashe junansu to akwai matsala babba.

Da yawa daga masu nazari suna alakanta wannan masifa da rashin adalci a cikin mulkin jiha da na kasa ta yadda ’yan tsiraru suka kwashe kudin al’umma suka bar su da hamma.

Ta bangare daya kuma sun zo suna amfani da wani bangare na al’ummar domin cimma burinsu. Su ba su taro da ahu, su ba su kayan shaye-shaye, su ba su makamai. Su kuma idan babu kasuwar siyasa sai su shiga kasuwar mutane da dabbobinsu. A kimiyyar siyasa kuma za a iya gaya maka duk kasar da ta ci gaba sai da ta zubar da jini a wata gaba na ci gabanta. Allah Ya kiyaye. A gaskiya dai asalin matsalar ita ce talauci da aka jefa mutane a ciki da rashin ilimi da  rashin aikin yi a cikin al’muma. Wato kamar bam ne da yake jira lokacin fashewarsa ta yi sai ya fashe.

Ta bangare guda kuma, akwai lalaci da cima-zaune da suka yi yawa a cikin al’umma saboda haka dole a yaki wadannan ’yan tagwayen. Haka na kafafen watsa labarai na talabijin da rediyo suna gyara amma fa wasu suna barna mai yawa. Maimakon mu samu kafa watsa labarai mai karfi mai iya barazana ga gwamnati idan ba ta yi daidai ba, a’a sai dai masu koya soyayya da badala wani lokci har da ta’addanci. A nan nake kira ga hamshakan ’yan kasuwarmu da su zuba hannun jari a harkar watsa labarai domin kare mutuncin al’umma, tarbiyyar ’ya’yansu da kare mutuncin Musulmi a kasa.

Gwamnati wajibi ne ta mai da hankali kan kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Al’umma wajiibi ne su hada kai su yaki miyagun cikinsu kafin su hallaka su. Masu hali dole su bayar da hakkin Allah tare da daukar nauyin marasa karfi daidai gwargwado. Masu ilimi dole su dage wajen wayar da kan al’ummarsu a kauyuka da birane. Wadannan su ne hanyoyin da insha Allahu za su samar mana da mafita mai dorewa. Allah Ya sa mu dace Ya albarkaci rayuwarmu.

Dokta Aliyu Dahiru Muhammad ya rubuto ne daga Jami’ar Bayero da ke Kano.