✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Basarake ya yaba wa fim din Wakili

Garkuwar Makarantar Zazzau Dokta Shamsuddeen Aliyu Maiyasin ya yaba wa fim din barkwancin nan Wakili. Fim din Wakili wanda ake ci gaba da haska shi…

Garkuwar Makarantar Zazzau Dokta Shamsuddeen Aliyu Maiyasin ya yaba wa fim din barkwancin nan Wakili.

Fim din Wakili wanda ake ci gaba da haska shi a sinima da Film House da ke Babban Kantin Ado Bayero a Jihar Kano ya samu yabon ne daga basaraken lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kalli fim din a Kano.

Dokta Shamsuddeen ya ce, fim din ya kyatar da shi matuka kuma ya nishadantar da shi, inda ya bayyana fim din a matsayin wanda ya cancanci yabo.

“Fim din Wakili, fim ne na barkwanci da yake dauke da darussa da dama. Duk da cewa da Harshen Hausa aka shirya fim dim, amma yana dauke da darussa da zai amfani dukkan bangarorin kasar nan, kuma za a koyi darussa da dama. Don haka nake ganin fim din ya cancanci yabo da kyautar girmamawa,” inji shi.

Daga cikin wadanda suke taka rawa a fim akwai jarumi Ali Nuhu da Sulaiman Bosho da Rabi’u Daushe da Hadizan Gambo da Aminu Momo da Falalu Dorayi da sauransu.

Shirin an tsara shi ne bisa tsarin barkwanci, wanda yake nuni a kan mugun halin wadansu gurbatattun shugabannin al’umma, inda suke amfani da matsayinsu suna aikata laifuffuka da dama a boye.

Falalu Dorayi ne ya shirya kuma ya jagoranci fim. Yanzu haka dai ana ci gaba da haska fim din a Kano, kuma za a haska shi a wasu jihohin nan ba da dadewa ba.