Daily Trust Aminiya - Basarake ya yaba wa fim din Wakili
Subscribe

Basarake ya yaba wa fim din Wakili

Garkuwar Makarantar Zazzau Dokta Shamsuddeen Aliyu Mai Yasin ya yaba wa fim din barkwancin nan Wakili.

Fim din Wakili wanda yanzu haka ake ci gaba da haska shi a Sinima da Film House da ke Babban Kantin Ado Bayero a Jihar Kano ya samu wannan yabon ne a wajen basaraken a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kalli fim din a Kano.

A cewar Dokta Shamsuddeen, fim din ya kyatar da shi matuka kuma ya nishadantar da shi, inda ya bayyana fim din a matsayin wanda ya cancanci yabo.

A jawabinsa, “fim din Wakili fim ne na barkwanci da yake dauke da darussa da dama. Duk da cewa da Harshen Hausa aka shirya fim dim, amma yana dauke da darussa da zai amfani duk bangarorin kasar, kuma za a koyi darussa da dama. Don haka ne nake ganin fim din ya cancanci yabo da kyautar girmamawa.”

Daga cikin wadanda suke taka rawa a fim akwai jarumi Ali Nuhu da Sulaiman Bosho da Rabiu Daushe da Hadizan Gambo da Aminu Momo da Falalu Dorayi da sauransu.

Shirin an tsara shi bsa tsarin barkwanci, wanda yake nuni a kan mugun halin wasu gurbatattun shugabanni al’umma, inda suke amfani da matsayinsu suna aikata laifuka da dama a boye.

Falalu Dorayi ne ya shirya kuma ya jagoranci fim.

Yanzu haka dai ana ci gaba da haska fim din a Kano, kuma za a haska shi a wasu jihohin nan ba da dadewa ba.

texem
More Stories