Categories: Ta'aziya

Bashir Musa Liman: Ba rabo da gwani ba….

Daga Allah muke kuma zuwa gare Shi za mu koma! Wannan kalami ne ya fito daga bakina, lokacin da Editan Jaridar Aminiya, Malam Salihu Makera ya kira ni a waya, ya sanar da ni cewa dan uwanmu, abokin aikinmu, Malam Bashir Musa Liman ya rasu a sanadiyyar hadarin mota.

Malam Makera ya kira ni ne a ranar Asabar da ta gabata (10-08-2019), wato ranar Jajibirin Babbar Sallah, daidai misalin karfe 5:30. Ya bayyana mIni a takaice yadda al’amarin ya faru, cewa marigayin ya tuka motarsa daga Jos, ya kama hanyar zuwa mahaifarsa, Jama’are domin gudanar da Babbar Sallah a can. Allah cikin ikonSa kuma ya gamu da hadari, wanda ya kasance ajalinsa.

ADVERTISEMENT

Tun daga lokacin nan na rika jimamin babban rashin da muka yi na haziki kuma zakakurin marubuci, dan jarida kuma masanin kimiyya.

Na fara sanin marigayi Bashir Liman ne tun wajajen shekarar 2009, shekara uku da fara wallafa jaridar Aminiya. Kasancewata Editan Shafin Adabi da Dandalin Nishadi na jaridar a lokacin, Malam Bashir kan aiko da rubuce-rubucensa, musamman kasidu da tsokaci da suka danganci wadannan shafuka.

ADVERTISEMENT

Ya kasance kwararre a rubutun Hausa, sannan ga shi da fasahar iya tsara labarun kirkira. Haka kuma gwani ne wajen nazari da bincike, inda yakan dauki maudu’i ya yi nazari a kansa, kafin wani lokaci ya hada maka kyakkyawan rahoto.

A wannan fannin, na dade ina karanta wani rubutu da ya yi wanda ya shafi rubutattun wakokin Hausa. Tun kafin ya zama ma’aikacin jaridar Aminiya, yakan jajirce wajen turo sakonnin da suka hada da mukaloli a fannoni daban-daban. Haka kuma, tun daga lokacin na saba da karantawa da tace wadannan rubuce-rubuce nasa da muke wallafawa a Aminiya.

Idan ya bushi iska, kawai za ka ji ya kira ka a waya, inda bayan ya gaishe ka, zai ci gaba da bayanin da yake so. Tun da muka fara mu’amala da Bashir, kafin ma ya fara aiki da Aminiya a shekarar 2013, bai taba kirana da sunana ba, duk kuwa da cewa sunanmu daya da shi. Yakan kira ni da “Oga” a yayin da ni kuma nake kiransa da lakanin “Diddigi” – lakanin da ya sanya wa sunan akwatinsa na I-mel.

A sanadiyyar irin wannan gaisawa da muke yi ta waya ce ta sanya ya zama daya daga cikin ma’aikatan jaridar Aminiya. Yaya abin ya faro? Wata rana ne ya aiko da wani sharhi game da ’yan fim din Kudancin Najeriya (Nollywood), lokacin yana Hidimar Kasa a Delta. Mun yi magana da shi, inda ya nuna sha’awarsa ta zama dan jarida, duk kuwa da cewa ba wannan fannin ya karanta ba a makaranta. Shi ya yi digiri ne a fannin Kimiyyar  Duwatsu da Ma’adinai (Geology), amma yadda yake rubutu da Hausa, kai ka ce fannin da ya karanta ke nan.

Ba zan mance ba, a lokacin akwai gurbin da ake bukatar a cike a jaridar Aminiya kuma ana son a dauki wanda ya kware a rubutun Hausa. Shi ne na shaida masa cewa idan har yana son aikin, zai iya rubutowa, mu kuma sai mu ba da shaidar cewa ya cancanta a zahiri, domin irin rubuce-rubucen da yake aiko mana na kashin kansa sun isa shaida.

Matsala guda aka kusa samu, domin kuwa a lokacin bai kammala hidimar kasa ba, duk da cewa saura kadan. Duk da haka na ba shi shawarar cewa ya rubuto bukatarsa ta son aikin jarida a Aminiya. Kuma na ce ya ci gaba da turo mana da rahotannin ’yan fim da mawaka na Kudancin Najeriya. Bayan ya rubuto da takardar, ni da Malam Salihu Makera wato Edita na yanzu muka yi masa shaidar cewa zai iya aikin, muka gamsar da shugabannin gidan cewa idan aka dauke shi ba za a yi da-na-sani-ba.

Malam Bashir ya samu aikin, ya zama Dan Rahoton Jaridar Aminiya, amma da ya zo sai aka ajiye shi a Hedikwata, a nan Abuja. Tun daga lokacin nan muka ci gaba da aiki tare cikin mutunci da karimci ga juna.

A wurin aiki, Bashir ya kasance jajirtacce wanda ba ya gajiya kuma ba ya saba duk aikin da aka ba shi. Cikin lokaci yake kammala shafukansa. Wani abin a yaba masa shi ne, bai tsaya ga Aminiya kadai ba, yakan rubuta rahotanni da labarai ga sauran jaridun Ingilishi na kamfanin, musamman ma Daily Trust (Saturday). Ya kware wajen kawo rahotannin ’yan fim da mawakan Hausa da aka fi sani da lakanin Kannywood.

Malam Bashir mutum ne mai ladabi da biyayya, mai barkwanci da nisahdantarwa. Kullum bakinsa za ka ga kamar gonar auduga, wasai yake cikin murmushi. Idan kana zaune da shi, da wuya ka ga fushinsa. Ko ka bata masa rai, da wuya ka gane fushinsa.

Matashi ne shi mai cike da lafiya, amma halayensa na manya ne. Mutum ne da ya bambanta da matasan zamani, domin kuwa ba ya almubazzaranci da nuna homa. Yakan fitar da kudinsa ya sayi sutura mai tsada, amma ba za ka gan shi da suturar tsiraici ta yaran zamani ba.

Kirjina cike da alhini zan karkare ta’aziyyar nan da baitoci 11 da nufin tunawa da shi tare da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.

Ta’aziyyar dan uwa kuma aboki

Inna lillahi kalma tabbatatta,

Wa inna ilaihi raji’una ka jiya.

Allah Shi kadai Ke tabbata,

Shi Ya kadarta komai tun jiya.

Bashir namu Liman mai shifta,

Ya bar mu yau wayyo duniya.

Na kasa kuka domin kuntata,

Na tunani sai ido ya na mujiya.

Kamar yanzu ne fasihin ambata,

Ya kake “Ogana ka kwan lafiya?”

Ladabinsa Bashir ya wuce ambata,

Murmushinsa kullum bai gajiya.

Yaro a siffar jikinsa amma dakata.

Tunaninsa kaifi tamkar na manya.

Natsuwarsa tsaf ba ya wauta,

Tsarinsa yai kama da na Injiniya.

Aikinsa kullum in ya tarkata,

Gwanin sha’awa da kamun zuciya.

Yau ya fake sahibi mu mun kuntata,

Jarimi a fagensa mai kyan haliya.

Roko muke Jallah Ka ambata,

Sunansa a Aljanna makaukakiya.

. .

Recent Posts

Kirkiro Masarautun Kano: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci

Babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 14 ga Nuwamba 2019, a matsayin ranar da za a yanke hukunci…

1 hour ago

An yi arangama tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da Gandujiyya a Kano

Akalla mutum takwas ne suka samu raunuka yayin da aka lalata motoci 10 a yau Litinin lokacin da aka yi…

2 hours ago

Kotu ta daure direba kan zargin yi wa agolarsa ciki a Abuja

Wata Kotun lardi ta birnin tarayya da ke Garin Jiwa Abuja, ta bada umarnin tsare wani direba mai shekara 36…

5 hours ago

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

Al'ummar Karamar hukumar Igabi da ke a jihar Kaduna sun waye gari cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga suka…

5 hours ago

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

11 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

11 hours ago