Da Dumi Dumi

Bashir Sama’ila Ahmed: Fitaccen dan jarida ya kwanta dama

A ranar Lahadin da ta gabata ce da misalin karfe 10:30 na safe Allah Ya yi wa fitaccen dan jaridar nan Alhaji Bashir Sama’ila Ahmed rasuwa bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon wata biyu.

Da yake bayyani game da marigayin, abokinsa Makaman Ringim Babba Alhaji Ibrahim Mohammed ya bayyana marigayi Bashir Sama’ila Ahmed da cewa kwararren dan jarida ne wanda ya dade yana bada gudunmawa ga aikin watsa labarai. Ya ce marigayin kuma mutum ne mai basira da salon maigana.

Ya ce yana daya daga cikin ma’aikatan rediyo da talabijin a Kaduna, wadanda suke da hazaka da barkwanci, inda a cewarsa da wuya masu saurare su manta da shi musamman wasannin kwaikwayo da ya yi a Gidan Rediyon Arewa (NBC), kan inganta aikin noma da sauransu.

“Marigayi Bashir Sama’ila Ahmed ya shahara a wasan kwaikwayon aikin gona  inda ya shahara da kirarin Basafce Dan Malam Dogara na Kumato mai karan kamun kura.

Haka kuma suna da wani shiri da shi da Rabi’u Bako da ake kira da Gundumi Fasa Kwanya,” inji shi.

ADVERTISEMENT

“Marigayi Bashir Sama’ila Ahmed Allah Ya yi shi haziki mai basira kuma ba ya da girma kai, kuma ba ya saurin fushi, ballantana fada da mutane, kuma duk wanda ya san Bashir ya san Allah Ya yi masa baiwa na abubuwa da yawa, domin kusan duk abin da ya sa a gaba za ka ga ya yi fice, kuma ya yi nasara a kansa.

Kuma mutum ne da bai daukar raini da wulakanci, kuma kwarerarsa ta sa Shugaban Gidan Rediyon Najeriya na Kaduna a lokacin, Alhaji Dahiru Modibbo yake matukar kaunarsa,” inji shi.

Shi ma da ya ke mika ta’aziyarsa, Alhaji Rabi’u Bako ya ce abokin aikinsa ne ta fanni biyu, “Mun yi aikin gidan rediyo tun daga farko har zuwa 1985. Daga nan kuma da na shiga siyasa aka nada ni Kwamishina Watsa Labarai, shi kuma a lokacin yana Babban Sakataren a Ma’aikatarmu, sai muka sake shakuwa da juna sosai, kuma tunda tun a farko mun yi aiki a bangarori da dama a lokacin da muke matasan ma’aikata,” inji shi.

Marigayi Bashir Sama’ila Ahmed ya yi aiki a Gidan Radiyo da Talabijin na Jihar Kaduna, (RTK) wanda ya koma Rediyon Najeriya na Kaduna a yanzu.

Marigayin ya zama Babban Sakatare a Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar Kaduna, inda a nan ne ya yi murabus daga aiki.

Marigayi Bashir Sama’ila Ahmed ya rasu yana da shekara 73, ya bar mata daya da ’ya’ya biyar. Kuma tuni aka yi jana’izarsa a Zariya.

Share