✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Basillar barden bindigar Bature

Babbar bulala Burgar busa badujala Baza bezar benun balbela Birgimar bambamin begila   Hakika cuta na da illa Mai ciwo na zubar hawayen kwalla Jikin…

Babbar bulala

Burgar busa badujala

Baza bezar benun balbela

Birgimar bambamin begila

 

Hakika cuta na da illa

Mai ciwo na zubar hawayen kwalla

Jikin jikkatar wahala

Gabbai na cikin sasarin talala

Don ba walwalar sakata a wala

 

Cututtuka na sa kasala

A shiga halin kila-wa-kala

Majinyata a halin ko’in-kula

Tabahuwar ta-molar tukin tuwon tula

Majinyaci bai rumurmutsar ’yar sala

 

Tunkarar tarin lala

Don yana haifar da lalala

Majinyata na ta wahala

Cuta ta shage kwala

Kuful-kuful majina na ta malala

 

Farfajiyar bokan Turai

Likitocin kwarai

Malaman jinya tarai-tarai

A tarairayi rai

Jajircewar jinyar jarirai

 

Barden bindiga

Bugi-in-buga

Bangaje banga-banga

Ba burga

Bambamin jan daga

 

Cuta ta ruga

Zazzabin zogin zuga

Farankama ta zaga

Amai zawo an tsuga

Basilar larura ta sa mamunga

 

Rigakafi

Rigar-kafi

Ruge-rugen ragon rafi

Rarrafen rankwafawar rufi

Ratattakar jikin mai korafi

 

Kunzugun kazanta

Kamuya-muyar karanta

Karfa-karfan kafafar karata

Kumbiya-kumbiyar kukuta

Karafan kundumbalar kankanta

 

Uwar jiki ta samu tabi

Gamagarin gabobi

An game su da kwabi

Ana ta maganin ciwon kwibi

A sasaba ai ta sabi

 

Baraden tsuntsayen sama

Ba su da dama

Gwaraza masu himma

Cuta su fyadeta sui jima

Jaruman jarma

 

Ina bakon dauro

Matukar ka duro

Lallai za ka sha kyauro

Basillar larura tai ma kwarkwaro

Lumanar uwar jiki tai awarwaro

Sangen sargafe sauro

Sunkurun sagarftun soro

Sasarin kwararo-kwararo

Sirrin tunkarar taro

Samamen garkamar horo

 

A dabbaka ikirari Haurubja

Na dubun karamin laujen sili

Wato aiki da hankali

Kar a debi kudi ai fatali

Kar na-mujiya yai kwajaja

 

An yi takaddamar tababar Haurubja

A dubun silin karamin lauje

Wato kada wa cuta jauje

A bangajeta ta baje

Babu na-jan-jen ja-in-ja

 

Kashi sili babban lauje

Ckin dari aka ce da Maisaje

Ya taimaka wa mai kauje

Da wanda ya kuje

Har wadanda suka daddauje

 

Sai a daina na-janje

Ko ai ta yi wa mutum jaje

Mahukunta ban da gwabje-gwabje

Farfajiyar Bokan Turai aka ce a je

To wa zai je

 

Danmagori

A sarrafa magungna nagari

Ingancinsu ya fito sarari

Kar a jefa jama’a garari

Jikon ruwa da kwayoyi curi

 

Tanadin tunkarar larura

Jinya sai da allura

Jami’ai ai ta lura

A dubi mai fama da mura

Har jiki ya sarara

 

A dai kafa tubali

Ginin gyaran hali

A yasar da karairayin kyalkyali

A datse ciwo da kansakali

Wannan shi ne rubutun wasali

 

A kyautata muhalli

Majinyaci mai hali

Ko marar hali

Su samu falalen fili

A tallafa ba feleken fi’ili

 

Farmakin fama

Samamen shammatar sammatsin sama

Baraden bindigar dagar dama

Janjamin jan takaddama

Tungar takun takama

 

Huwe

Hargitsin hawaye

’Ya’ya da iyaye

Abokai da kawaye

Ba masaniyar shirin Huwe

 

Talakawa a ba su kati

Rajistar shigar tanti

Na yanke cuta da balati

Na karkara a daina harbatta-mati

So ake ku samu sabati

 

Kowa ya gana da bakin Bature

Lalura duka a ture

Daga cuta akan murmure

A ci moriya a more

Ai tsallen badake a dire

 

Mutanen maraya

Farfajiyar Bokan-Turai ta tarayya

Shawarar warakar warwara a biya

A firfito ka da a buya

Mui gaba-gaba kar mui baya

 

Talaka ya samu gata

Na karkara da Belin-auta

Sai a daina wauta

Magani ne za a byar kyauta

Mamugunta kar ai sata

Tarayyar Ifirikiyya

Tai tattaunawar togaciya

Tarairayar tankiya

Tattalin tulin toliya

Torokon tumbudin tsiya

 

Damar daukar dawainiya

Danne damuwar danniya

Cakwaikwaiwar carin curiya

Kambama kakarin kariya

Birgimar bilinbituwar baudiya

 

Hakika na baje na-mujiya a farfajiyar bokan Turai ta zaratan zakakuran  baraden bindigar samatsin samamen saman shawagin shammatar shamuwa, inda na yi arba da zakakuran zaratan jami’an kula da lullumin lumanar uwarjiki da jami’an jigata cutar da ta addabi majinyata, wadanda aka wadata su da dimbin na’urorin nunin nakaltar zogin zungurar zamani, don jin dadin sauke nauyayye-nauyayyen da suka ta’allaka da ayyukansu.

Tabbas cuta na da illa, domin masu faman ciwo kan zubar da hawaye har  kwalla ta yi ta kwarara a jikin mai fama da wahala, tunda ai gabbobi na cikin sasarin talalar rashin walwala ballantana a sakata a wala.

Watakila, wannan dalilin ne ya sanya a kowace cibiyar ciccibar cin dunun danne dawurwurin dumuiniyar caccakar carin cututtukan lulawar laulayin uwarjiki ta baraden bingidar Haurobiya, wadda aka tanadi basillar babbar bulala burgar busa badujala ke da inganci, don kawar da balbalin bala’in badalar birgimar bankade badalar garkuwar gambun gararambar garnakakin gundumin gwarzon gwaraza. Kai in gajarce wannan batu na hango BASILLAR BINDIGAR BARADEN BIDIRIN BOKAN BATUREN TURAWAN TURAI, mai tattara turakun tarayyar tarairayar rai da malaman jinyar kwarai.

Idan har an yi wa masu yi wa kasa garkuwa katafariyar cibiyar cacume cututtuka, to gama-garin al’umma na da matukar bukatar kwatankwacin irin wadannan cibiyoyin, don kowa ya rabauta ka da a shiga ragaita, tunda sananen lamari ne cewa: Cututtuka na sa kasala, har a shiga halin kila-wa-kala, kuma a rika nuna wa maajinyata halin ko’in-kula, ga tabahuwa na tukin ta-molar tuwon tula, ga shi majinyaci ba ya iYA rumurmutsar ’yar sala. A irin wannan yanayi, ta yaya za a tunkari tarin lala mai haifar da lalala da matsananciyar wahala da ke sanyawa cuta ta shage wa mutum kwala, ya yi ta kuful-kuful majina na dalala?

Babu mafita sai ruge-rugen rugumniyar rarumar ragon rafi ko da yin rarrafen rankwafawar rufin ratattakar jikin mai korafi a lullube mutum da rigar-kafin rigakafin cututtuka masu bazuwar buzuzu buzu-buzu. Kuma a yunkura wajen ganin cewa kariyar kyautata karkara ba ta zamo kakarar kassara kararen Huwe na hauhawar hallarar hawaye. Kula da ingancin uwar jiki ko dai babu a hallarar HUWE ne?

Tarayyar Ifirikiyya ta taba tattaunawar togaciyar tarairayar tankiyar tattalin tulin taraliyar tulun tunkarar tumbudin tsiwar tsokacin tsiya-tsiya, don tsare-tsaren tsayuwar tsare gida, ta yadda cututtuka za su daina yi wa al’umma kaka-gida.

Tun cikin shekara ta dubu karamin lauje da sili aka yi gagarumin cincirindon kasashe masu ruwa da tsaki, karkashin Tarayyar Ifirikiyya, har ma da dandago-dago, inda aka bibiyi kadin yadda ake kula lullumin lumanar uwar jiki a birnin Haurubja

Cikin wata Afarinlilon shekara ta dubu karamin lauje da sili aka gudanar da wannan gagaraumin cincirindon, amma zuwa shekarar dubu karamin lauje da sili da manuniyar sama kasa guda ta cimma muradi, sannan kasashe karamin lauje da manuniyar sama sun kara kwazon kula da uwar jiki, yayin da rukunin kasashe sili da sili suka yi sako-sako da cin kasa kasa-kasa warwas.

Abin bin bahasi, shin ko Haurobiya na cikin jerin kasashen tarairayar tarayyar Ifirikiyya da suka kai ga gacin gajiyar alwashin da aka cimmawa wajen kula da lullumin lumanar uwarjiki? Tabbas tana ciki. Idan kuwa haka lamarin yake, lallai akwai bukatar a yi wa gama-garin Haurobiyawa katafariyar farfajiyar Bokan Turai ko da a kauyen kayau, wadda in an kwatanta kimar aikinta, ko a kasashen ketare iyakar agajin da za a iya bai wa majinyaci ke nan.

’Yan makaranta da daukacin masu falle shafukan sadarwa a Haurobiya, lallai mu himmatu ka’in da na’in wajen ganin Gwamnatin Haurobiya ta yunkura don cimma manufar ikrarin Haurubja na shekara ta dubu karamin lauje da sili, wajen aiki da hankali, don tarairayar uwar jikin mai hali da mara hali. Irin wannan namijin kokari zai iya kasancewa BELIN-AUTA ga al’ummar kasar nan. Kodayake Gwamnati ta wassafa tsarin tallafin inganta uwarjiki mazaunan karkara (a kundin watsattsaken warkoki), amma har yanzu dai abin sai dai a ce, ‘SHAGALIN SHARBAR SHAWARMAR SHIRWA SHIRU SHIRIM!

Haurobiyawa, a kara kwazon kyautata muhalli, ta yadda majinyaci mai hali ko marar hali za su wadatu da falalen filin tallafawa ba tare da fankamar fariyar  feleken fi’ili ba.