✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun Takaita Haihuwa: Matsalar Najeriya rashin tsari ne ba yawan al’umma ba

A ’yan kwanakin nan, ana ta kai komo dangane da batun tazarar haihuwa ko takaita haihuwa a Najeriya. GIZAGO (08065576011) ya bibiyi al’amarin, inda ya…

A ’yan kwanakin nan, ana ta kai komo dangane da batun tazarar haihuwa ko takaita haihuwa a Najeriya. GIZAGO (08065576011) ya bibiyi al’amarin, inda ya bayyana mahangarsa dangane da yawan al’umma a Najeriya:

A Najeriya, an dade ana ta kai kawo dangane da al’amarin yawan jama’a. Akalla, kowace gwamnati kan yi tsare-tsare dangane da yadda za ta tafiyar da al’umma, musamman ma wajen samar da kyakkyawan yanayin tafiyar da rayuwa, wanda ya shafi tattalin arziki, ilimi, lafiya, muhaalli, tsaro da sauransu. Babbar matsalar ba ta samar da tsarin ba ce kuma ba ta yawan al’ummar da ke karuwa a kullum ba ce. Babbar matsalar ta takaita ne ga tafiyar da tsarin da ya dace sau da kafa.

A farkon makon jiya ma, an ruwaito Ministar Al’amuran Kudi ta Najeriya, Dokta Zainab Ahmed Shamsuna tana magana dangane da kawo tsarin da ya shafi takaita haihuwa, domin samar da tsari mai kyau game da tattalin arzikin kasa. Kamar yadda ta ce a cikin harshen Ingilishi, “Mun ankara da cewa hauhawa da karuwar jama’a ne babban kalubalenmu dangane da tafiyar da tattalin arzikin kasa. Ba mu ce Gwamnatin Tarayya za ta kayyade ‘ya’yan da mutum zai haifa ba. Gwamnati tana tuntubar sarakunan gargajiya da malaman addini domin su ilimantar da mutanensu dangane da tazarar haihuwa, domin su rika haihuwar adadin ‘ya’yan da za a iya kulawa da su sosai.”

Ni kuwa na ce, ba fa yawan al’umma ne ke haifar da matsin tattalin arziki ba, komai yawan al’umma, muddin aka samu tsarin gudanarwa mai kyau da shugabanci mai kyau, yawan jama’a rahama ne. Wani abin da ya kamata mu fahimta shi ne, duk wata kasa da ka ga ta ci gaba a duniya, babban abin da ya ba ta wannan shi ne yawan al’umma. A tarihin Turai, yawan al’umma ne ya yunkurar da su suka samu daukaka a duniya ta fuskar tattalin arziki da kere-kere. A tsakanin shekarar 1760 zuwa 1840, tumbatsa da yawan al’umma a Turai ne ya sanya suka maida hankali wajen kere-kere da sarrafe-sarrafe, suka bazama ko’ina a cikin duniya, musamman Afrika domin neman kasuwa da kayan sarrafawa.

A China, yawan al’umma ne ya ingiza su suka farka, suka yi nazari da karatun-ta-natsu, a tsakanin shekarar 1958 zuwa 1961 suka maida hankali kacokan kan noma da sarrafe-sarrafe da kere-kere. Sai da suka rufe kasarsu na tsawon shekaru daga shigo da wani abu na kira ko noma. Da kansu suka rika kera duk wani abu da suke bukata, suka rika noma duk wani abinci da suke bukata. Ta kai ga a yau China ta fi karfin abinci da duk wani abin kere-kere, sai dai ta fitar waje ta sayar kuma ita ce ta farko a duniya wajen yawan al’umma.

A Jamus, akwai lokacin da suka yi tsarin kayyade haihuwa, amma ba su ji da dadi ba, domin kuwa sai da aka samu wani lokaci, tsofaffi sun fi matasa yawa. Dole uwar na ki, dole suka sassauto. A yanzu, duk magidantan da suka samu haihuwa, har wani tallafi ake ba su, saboda yawan al’ummar suke nema.

Kasar Indiya, ita ce ta uku a yawan al’umma a duniya amma a yau tana daya daga cikin kasashe masu tashe ta fannin tattalin arziki, kere-kere da bunkasar ilimi. Me ya ba su wannan? Sun samar da tsarin gudanarwa mai kyau ga al’umma, sun sanya kishin kasa da burin ciyar da ita gaba.

Mu a nan Najeriya, ana hasashen cewa muna da adadin akalla yawan mutane miliyan 200 ne, kuma mu ne mafi yawa a Nahiyar Afrika. Allah Ya albarkace mu da faffadar kasar noma mai kyau. Muna da ma’adinai da sauran albarkatun karkashin kasa masu dinbin yawa. Muna da albarkar man fetur da iskar gas. Kasar China ba ta da irin wannan albarkar, haka ma kasar Indiya amma sun ninninka mu yawa fiye da kima. To yaya aka yi su yawan al’ummarsu bai hana su ci gaba ba? Saboda sun dauki matakin da ya dace, sun samar da tsarin tafiyar da al’umma mai kyau da dacewa, sun sanya kishin kasa da na al’umma a tafiyar da al’amuransu.

Mu kanmu a nan Najeriya, idan har za a samar da kyakkyawan tsari, za mu iya ririta yawan al’ummarmu domin mu ci gaba kuma mu bunkasa a duniya. Muna da yawan al’umma, don haka muna da kasuwa ta kai tsaye ga duk abin da muka sarrafa. Muna da wadatattar kasar noma, wacce za ta ba mu damar noma duk abin da muke bukata, har ma mu sayar kasashen waje. Idan har shugabanni za su daina sace-sacen dukiya suna jibgewa kasashen waje, idan har za a yi amfani da dukiyar kasa wajen samar da ingantattun makarantu da ingantattun kamfanonin sarrafa albarkatun kasa, babu shakka za mu samu nasara.

A yau a Najeriya, mutum guda sai ya sace dukiyar da mutum miliyan goma za su iya amfani da ita, daga shi sai ‘ya’yansa biyu ko uku. Sai mutum guda ya kimshe abincin mutum miliyan goma a gidansa shi kadai. Sai mutum guda ya girke motocin alfarma guda 20 shi kadai. Sai mutum guda ya mallaki jiragen shiga na alfarma shi kadai. Daidai da Kansila, ‘ya’yansa na kasar waje suna karatu, Daidai da karamin ma’aikaci a NNPC, idan matarsa ta tashi haihuwa kasar waje zai nufa. Shin ta yaya za a ci gaba?

Ko addinance ma, yawan al’umma ba shi ke gadar da talauci ko rashi ba. An samu hadisin da ke cewa, Manzon Allah (saw) ya ce, abincin mutum daya, ya ishi mutum biyu, abincin mutum biyu, ya ishi mutum uku… Hikimar da ke cikin wannan kalamin ba ta tsaya ga abinci kadai ba, za ta iya tasiri a dukkan al’amuranmu na rayuwa, kamar muhalli, sutura, abin hawa da sauransu.

Ya kamata gwamnatocinmu, attajiranmu, malamanmu da masananmu su yi nazari su canja tsarin gudanarwar kasar nan. A daina sata da almundahana. A hana almubazzaranci da dukiyar kasa. A maida hankali wajen samar da bunkasasshe kuma kyakkyawan tsarin ilimi. A maida hankali wajen noman zamani, wanda zai iya samar da isasshen abinci, ya samar wa dinbin matasa aikin yi. A maida hankali wajen binciken kimiyya da kere-kere. Malaman addini su maida hankali wajen cusa tsoron Allah ga mabiyansu da samar da hadin kai tsakanin al’umma.

Allah Ya Taimaki Najeriya!