✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan binciken DSS Oshiomhole ya ziyarci Amurka

Shugaban jam’iyya mai mulki ta APC na kasa Kwamred Adams Oshiomhole ya fita daga kasar bayan da hukumar tsaron farin kaya DSS suke tuhumarsa a…

Shugaban jam’iyya mai mulki ta APC na kasa Kwamred Adams Oshiomhole ya fita daga kasar bayan da hukumar tsaron farin kaya DSS suke tuhumarsa a ranar Lahadi da Litinin. Kamar yadda majiyarmu ta bankado daga wani babban dan jam’iyyar.

Hukumar DSS da hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta Najeriya, EFCC na tuhumar shugaban jam’iyyar ne akan karbar cin hanci lokacin gudanar da zabukan fidda gwani da aka yi na APC.

Jihohin da ake zargin karban sun hada da: Imo da Ogun da Neja da Zamfara. Sannan akwai zargin hakan a jihohin  Kaduna, Bauchi, Adamawa, Delta da Kuros Riba.