✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan da sojojin Chadi suka fatattaki ’yan Boko Haram

Mutane a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya sun jinjinawa sojojin kasar Chadi wadanda rahotanni suka ce sun kashe mayakan Boko Haram da dama…

Mutane a jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya sun jinjinawa sojojin kasar Chadi wadanda rahotanni suka ce sun kashe mayakan Boko Haram da dama a makon jiya a yankin Tafkin Chadi.

Masu bin diddigin alamuran dai sun ce Shugaban Idris Deby ne da kansa ya jagoranci sojojin wajen kaddamar da hare-haren don kakkabe ’yan Boko Haram daga yankin kasar sa.

Ibrahim Uba Yusuf, wani malami a Tsangayar Koyon Aikin Jarida a Jami’ar Maiduguri, kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, ya ce abin akwai ban sha’awa.

“Hakika sojojin Chadi sun taka rawar gani saboda yadda a dan kankanin lokaci suka fatattaki ’yan Boko Haram”, inji Malam Ibrahim.

Wani mazaunin jihar ta Borno Ali Suleiman Abubakar kuwa, kira ya yi ga shugabannin Najeriya su yi koyi da na Chadi.

“A gaskiya idan har yadda muke ji a kafofin yada labarai gaskiya ne, to sojojin Chadi sun ciri tuta idan muka duba yadda cikin kankanin lokaci aka karkade Boko Haram a yankin kasar tasu; kuma Shugaba Idiris Deby ya cancanci a yaba masa, don da a ce shugabanninmu na Najeriya da Nijar za su yi koyi da shi, to da yanzu babu ’yan Boko Haram”, inji Malam Ali.

Rahotanni sun ce gwamnatin Chadi ta kaddamar da hare-haren na ramuwar gayya ne bayan da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kashe wasu sojojin kasar.

Ko da yake wasu bayanai sun nuna cewa adadin ’yan Boko Haram din da sojojin Chadi suka kashe sun haura  100, babu tabbacin hakan a hukumance.

Wata majiya ta shaidawa Aminiya cewa sojojin Chadin sun shigo har garin Dikwa, mai tazarar kilomita fiye da 40 daga iyakar Najeriya da Kamaru ta gabas.

Sai dai kuma kasancewar babu hanyoyin sadarwa a garin har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu wata majiya ta daban da ta tabbatar da hakan ba.

Amma dai a wata sanarwa da ya fitar a garin Ngamdu ranar Juma’a, Mukaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Kanar Sagir Musa, ya ce babu wani yanki na kasar nan da ke hannun sojojin Chadi.

Kanar Musa ya ce akwai rundunar hadin gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da na kasar Chadi mai shalkwata a N’Djamena, don haka ana aiki tare, kuma ba gaskiya ba ne cewa sojojin Najeriya ba sa nan a wuraren da sojojin Chadi ke fafatawa da ’yan Boko Haram.

Kakakin na Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ya kuma ce kalaman da wani jami’in Rundunar Sojin Kasa ta Chadi Kanar Azem Aguna  wanda suka kwace daga hannun ‘’yan Boko Haram ba gaskiya ba ne.

Rahotanni dai sun ce sojojin kasar ta Chadi sun fatattaki mayakan Boko Haram daga dukkan sassan kasarsu zuwa wasu yankuna a Najeriya, da nijar da kamaru.