✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan dakatar da shi: Oyinlola ya yuntura don fara aiki a matsayin Sakataren PDP

Duk da dakatar da shi da Jam’iyyar PDP ta yi Sakataren Jam’iyyar na tasa da kotu ta mayar, Yarima Olagunsoye Oyinlola ya rubuta wa jam’iyyar…

Duk da dakatar da shi da Jam’iyyar PDP ta yi Sakataren Jam’iyyar na tasa da kotu ta mayar, Yarima Olagunsoye Oyinlola ya rubuta wa jam’iyyar yana sanar da ita ta dauka shi ne Sakataren Jam’iyyar.

A takardar da ya aike ga Mashawarcin Jam’iyyar kan Harkokin Shari’a dauke da kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2013, tare da kwafen hukuncin kotu da ya mayar da shi kan kujerarsa, ya nanata cewa shi ne kadai mutumin da yake da ’yancin sanya hannu a kan duk takardun da jam’iyyar za ta aika wasu wurare daga sakatariyarta a matsayinsa na babban jami’in gudanarwa kuma babban akantanta.
Yayin da yake kiran kansa da Sakataren Jam’iyyar PDP na tasa Oyinlola ya nemi jam’iyyar ta girmama umarnin kotun.
A wani labarin kuma Jam’iyyar PDP ta rubuta wa Hukumar Zabe ta tasa (INEC) wasita domin sanar da ita cewa ta dakatar da Oyinlola da kotu ta mayar a matsayin Sakatarenta na tasa da kuma wasu jami’an jam’iyyar uku.
Wata takarda da ta fito daga Sakataren Labarai na Jam’iyyar ta tasa Olisa Metuh a ranar Talata ta ce Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar a wata takarda mai kwana wata 12 ga Nuwamba, 2013 da Shugabanta na tasa Alhaji Bamanga Tukur ya sanya wa hannu, ya sanar da INEC game da dakatar da Oyinlola da sauran mutum uku.
PDP ta zargi jami’an da yin ayyukan zame tafar jam’iyyar lamarin da ta ce ya saba wa tsarin mulkin jam’iyyar.
Jam’iyyar PDP ta ce dakatar da jami’an hudu ya gudana ne a tartashin ikon da take da shi a tartashin sashi na 57 (3) na tsarin mulkin PDP na 2012 (da aka gyara), kuma domin amfanin jam’iyyar da mambobinta.
A ranar Litinin ce Jam’iyyar PDP ta dakatar da Yarima da Shugaban sabuwar PDP Alhaji Kawu Baraje da Mataimakinsa Mista Sam Jaja da kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Shiyyar Arewa maso Yamma Jakada Ibrahim Kazaure, a wani abu da ake ganin yunturi ne na hana Oyinlola komawa kan kujerarsa bayan Kotun daukaka tara ta Abuja ta yanke hukunci mayar da shi kan mutaminsa.