✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan Hajji sai kuma me? (1)

Masallacin Annabi (SAW), Madina Fassarar Salihu Makera Hamdala da taslimi. Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku bi Allah da takawa, lallai yi maSa takawa shi…

Masallacin Annabi (SAW), Madina

Fassarar Salihu Makera

Hamdala da taslimi.

Bayan haka, ya ku Musulmi! Ku bi Allah da takawa, lallai yi maSa takawa shi ne mafi ribar kasuwanci. Ku guji saba maSa, hakika duk bawan da ya yi sakaci da umarnin Allah, ya wulakanta shi ya tabe. “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku bi Allah da takawa, ku fadi magana madaidaiciya. Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta zunubanku. Kuma wanda ya yi da’a ga Allah da ManzonSa, to, ya rabauta da babban rabo mai girma.” (K:33:70-71).

Ya ku Musulmi! Lallai bautar bawa ga Ubangijinsa ita ce alamar tawalin’unsa da dalilin gaskiyarsa da tambarin mika wuyansa. Bauta ita ce martaba ta fili da daukaka abar alfahari. Bauta ita ce mafi darajar mukami, mafi matukar daukaka, kuma mafi daukakar martabobi da darajoji.

Ya ku Musulmi! A ’yan kwanakin nan ne mahajjata suka kammala wata ibada daga cikin manyan ibadoji, suka kammala aikin kusanci ga Allah daga cikin manyan ayyukan kusanci gare Shi. Sun kusanci Allah kamar allura da zare a wurin Mikati, sun zubar da hawayen tuba a filin Arfa, suna masu tsoro kan gazawarsu da sabonsu. Saututtuka sun dagu don nuna bukata zuwa ga Allah a dukkan harsuna. Rayuka sun gangara zuwa Muzdalifa don kwana, sannan jama’a ta yi tururuwa zuwa jifar jamrori da Dawafi ga Dakin Allah Mai daraja da yin Sa’ayi a tsakanin Safa da Marwa a cikin tafiya mafi ban mamakin tafiya da daga muryoyi mafiya dadi. Kuma a bayan haka sai suka fara komawa kasashensu suna masu farin ciki da abin da Allah Ya ba su daga falalarSa. “Ka ce da falalar Allah da rahamarSa, sai su yi farin ciki da wannan.” Shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa.” (K: 10: 58). Mafi alheri daga duniya da tarkacenta wadanda ba wasu abubuwa ne ba face rudi mai gushewa, makomarsu gushewa da rabuwa da su, jin dadi ne dan kadan, bijirowarsu don cutarwa ce, kuma su toshe hanyar tsira.

Don haka madallah da hajjinku ya mahajjat! Masu ibada suna da ladar ibadarsu da kokarinsu. Madallah gare su kan maganar Manzon shiriya (SAW) cikin abin da ya ruwaito daga Ubangijinsa Madaukaki: “Idan bawa ya kusance Ni da taku daya, Zan kusance shi da zira’i, idan kuma ya kusance Ni da zira’i, Zan kusance shi da kamu. Idan kuma ya zo Min yana mai tafiya, Zan zo masa ina mai sauri.” Buhari ya ruwaito shi.

Mahajjata Dakin Allah Mai alfarma, ku gode wa Allah kan ni’imar da Ya yi muku. Ku yi maSa hamdala kan abin da Ya ba ku, alherorinSa suna bibiyarku, kuna haduwa da  su, kyautarSa tana game ku, falalolinSa sun kammala gare ku, nafilolinSa sun cika. “Kuma abin da yake a gare ku na ni’ima, to, daga Allah ne.” (K:16:53). Da fadinSa (SWT) “Kuma idan kun kidaya ni’imar Allah, ba ku iya lissafa ta. Lallai ne Allah, hakika Mai gafara ne Mai jin kai.” (K: 16:18).

Mahajjata Dakin Allah Mai alfarma, ku yi zaton kowane abu  mai kyau daga Ubangijinku, ku yi kwadayi dukkan alheri mai yawa. Ku karfafa fatarku ga Allah wajen karbar Hajjinku da shafe abin da ya gabata na zunubanku. Hakika ya zo a cikin Hadisin Kudisi cewa: “Allah Madaukaki Ya ce: “Ina inda bawaNa yake zatoNa.” Shaikhani suka ruwaito.

Kuma an karbo daga Jabir (RA) cewa ya ji Annabi (SAW) kafin rasuwarsa da kwana uku yana cewa: “Kada dayanku ya mutu face yana kyautata zato ga Allah Mai girman Daraja.” Muslim ya ruwaito.

Ya ku Musulmi! Ya ku wadanda suka hajjati Daki Mai tsohon tarihi! Kuka zo daga kowane sako mai nisa, kuka yi talbiyya a kowane gefe mai nisa, ga shi kun kammala Hajjinku, kun cimma muradunku bayan kun tsaya a kan hai’arku kuka yi wadannan ayyuka, ga shi kuna ta shirin komawa gidajenku (kasashenku), don haka ku guji komawa zuwa ga cudanya da abubuwan da aka haramta da rungumar ababen kyama da gwamutsar miyagun abubuwa. “Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bayan tukka.” (K:16:92).

Ita ce wawiyar mace, doluwa, mai karancin hankali, ta wahala dare da rana wajen kula da gashinta, har sai da ya isa kitso, ya yi karfi, sai ta dawo tana yayyanke gashin, tana warware tukkarsa bayan ta wahala a kansa, ba ta ci gajiyarsa ba, face wahala. Don haka kada ku kasance kamarta, ku rusa abin da kuka gina, ku ko watsar da abin da kuka tara, ko ku warware abin da kuka kulla.

Mahajjata Dakin Allah, hakika kun bude sabon shafi fari mai haske a rayuwarku. Bayan Hajjinku kun sanya wata sutura mai tsarki marar dauda, don haka ku guji komawa ga aikata munanan ayyuka, ko bin hanyar hallaka ko ayyukan kazanta. Me ya fi bibiyar abu mai kyau da wani abu mai kyau! Me ya fi munin bibiyar kyakkyawan abu da mummuna!

Ya ku Musulmi! Lallai idan Hajji ya zama karbabbe za a ga sauyi ga ma’abucinsa, za a ga haske a rayuwarsa. An tambayi Hasanul Basri (Rahimahullah): “Mene ne Hajji karbabbe?” Sai ya ce: “Ka kara gudun duniya, kana mai kwadayin Lahira.” Domin haka Hajjinku ya kasance kariya daga dukkan abubuwa masu hallakarwa, ya hana ku barnace-barnace. Ya kara muku himma ga aikata alheri da aikata ayyukan kwarai. Ku sani lallai mumini ba ya da iyaka ga aikata aikin kwarai har sai ajalinsa ya riske shi.

Ya ku Musulmi! Me ya fi kyau ga a ce Alhaji ya koma ga iyalansa da kasarsa bayan kammala Hajji yana mai cike da kyawawan dabi’u da hankali mai yawa da natsuwa tabbatacciya da kamewa da dabi’a abar yarda da halaye masu girma! Me ya fi kyau ga a ce Alhaji ya komo daga Hajji yana mai kyan mu’amala ga matansa da mu’amala mai kyau da ’ya’yansa, yana mai cike da tsarkin zuciya, mai bin hanyar gaskiya da adalci da daidaituwa, wanda alherinsa da ke boye ya fi wanda ke bayyane. Duk wanda ya dawo daga Hajji da wadannan siffofi, hakika shi ne wanda ya amfana da aikin Hajji ya amfana da sirrorinsa da darussansa da tasirinsa.

Ya ku Musulmi! Lallai mahajjaci tun daga lokacin da ya fara talbiyya har ya kare Hajjinsa, duk ayyukan Hajjinsa da yankarsa dada sanin Allah ne, tunatarwa ce gare shi kan hakkokinSa da kebantar uluhiyyarSa Madaukaki da fahimtar cewa babu wanda ya cancanci ibada bayanSa, dada saninSa ne da tuna cewa Shi ne Allah Makadaici da rai ke mika wuya gare Shi, fuskoki suke juyawa gare Shi, kuma Shi ne kadai Wanda halittu ke nufi da bukata wajen neman bukatunsu da neman tsari daga abubuwan da suke ki da Istigasa lokacin bakin ciki. To yaya zai yi sauki ga Alhaji bayan haka ya sarrafa wani hakki na Allah kamar addu’a da istigasa da isti’ana da yanka da bakance zuwa ga waninSa? Wane Alhaji ne zai aikata wani abu daga cikin wannan shirki bayyananne da aiki mai muni?