✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan kashe al-Baghdadi: Ana farautar kusoshin Kungiyar IS

Ana ci gaba da kai samame kan manyan shugabannin Kungiyar IS a Siriya a wani abu da ke nuna gaggawar da ake yi na kawar…

Ana ci gaba da kai samame kan manyan shugabannin Kungiyar IS a Siriya a wani abu da ke nuna gaggawar da ake yi na kawar da kusoshin kungiyar.

Dakarun gamayyar mayakan SDF da ke kawance da Amurka, wadanda suka taka rawa wajen kawar da Shugaban Kungiyar IS, Abu Bakr al-Baghdadi da Kakakin Kungiyar, Abu Hassan al-Muhajir, sun ce an kai wasu jerin hare-hare a ranar Larabar makon jiya da nufin kawar da manyan shugabannin kungiyar, inda aka neme su a raye ko a mace.

Kakakin Mayakan SDF, Mustapha Bali, ya wallafa a shafinsa na tiwita cewa, “An yi nasarar kai wani samame tare da kama wadansu manyan shugabannin Kungiyar ISIS.” Ya ce wadanda ba a kashe su ba za a kama su, yana mai cewa laifuffukan da kungiyar ta IS ta aikata ba za su tafi a banza ba.”

A ranar Lahadi ne Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da cewa Al-Baghdadi “ya yi mutuwa irin ta karnuka,” a wani hari da dakarun Amurka na musamman suka kai a Syria.

Mutuwar jagoran Kungiyar IS, Abu Bakr al-Baghdadi ta zama nasara ga Shugaban Amurka Donald Trump da ke fuskantar kakkausar suka kan matakinsa na janye dakarun Amurka daga Arewa maso Yammacin Syria- da kuma kokarin kalubalantar binciken tsige shi da Jam’iyyar Democrats ke yi. Sai dai kawayen Amurka sun ce kisan al-Baghdadi ba yana nufin yaki da Kungiyar IS ya zo karshe ba ne.

“Al-Baghdadi ya kashe kansa da yaransa uku bayan ya tayar da bam din da ke jikinsa,” inji Mista Trump.

Babu wani sojan Amurka da ya rasa ransa sakamakon tashin bam din sai dai daya daga cikin karnukan sojojin Amurka ya raunata matuka.

Shugaban ya bayyana cewa fashewar bam din ya tarwatsa al-Baghdadi, kuma wani gwajin kwayoyin halitta da aka gudanar da wurin da lamarin ya faru ya tabbatar da cewa lallai shi ne ya mutu.

Martanin shugabanni kan  mutuwar al-Baghdadi?

Shugabanni a fadin duniya sun mayar da martani dangane da mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi inda da dama daga cikinsu ke cewa za a ci gaba da yaki da Kungiyar IS.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa sun ji dadi matuka tare da gamsuwa sosai lokacin da suka samu labarin an kashe Shugaban Kungiyar ta’adda ta Daesh Al-Baghdadi.

A sanarwar da Erdogan ya fitar ta shafinsa na tiwita ya yi bayani game da kashe shugaban na Daesh Al-Baghdadi.

Ya ce “Kashe Shugaban Daesh na nuni da wani mataki mai muhimmanci na hadin kanmu. Turkiyya da ta fi fuskantar matsaloli daga hare-garen Daesh, PKK, YPG da sauran kungiyoyin ta’adda, ta ji dadi da kashe Baghdadi da aka yi.”

Shugaba Erdogan ya nanata cewa hada kai waje guda don yaki da ta’addanci a duniya zai kawo wa kowane bangare zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Saudiyya ta jinjina wa Amurka kan abin da ya jawo kashe Shugaban Kungiyar IS Abu Bakr Al-Baghdadi.

Cikin wata sanarwa da kafar labaran kasar (SPA) ta fitar, wacce jaridar Saudi Gazette ta ruwaito ta ambaci wata majiyar Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar tana ce wa gwamnatin Saudiyya ta yi hakan ne bayan da Amurka ta sanar da kawar da Al-Baghdadi.

Sanarwar ta ce “Gwamnatin Saudiyya ta yaba wa namijin kokarin Amurka na fatattakar mambobin kungiyar ’yan ta’adda mai matukar hadari, wacce ta yi ta kokarin bata ainihin akidar Musulunci da Musulmi a fadin duniya. Kungiyar da ta yi ta aiwatar da miyagun ayyuka da suka saba wa darajar dan Adam a kasashe da dama da suka hada da Saudiyya.”

Majiyar ta ce Masauratar Saudiyya na ci gaba da kokari tare da kawayenta da Amurka ke jagoranta wajen dakile ta’addanci, da toshe duk wata kafar yin sa da kuma yin fito-na-fito da masu akidar.

Firayi Ministan Birtaniya, Boris Johnson ya bayyana mutuwar al-Baghdadii a matsayin “Wani muhimmin abu a fadan da ake yi da ta’addanci amma fadan da ake yi da IS bai kare ba.’’

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana wannan ci gaba a matsayin wata “Babbar nasara’’ da aka samu kan IS amma “za a ci gaba da yakarsu har sai an tarwatsa kungiyar ’yan ta’addar.’’

Sojoji na musamman da suka kai samamen sun shafe kusan sa’o’i biyu a wurin suna tattara bayanai kuma sun samu bayanai da abubuwa sosai inji Trump.

A ranar Lahadi mayakan Kurdawa na SDF sun bayyana cewa mai magana da yawun Kungiyar IS Abu al-Hassan al-Muhajir wanda na hannun damar al-Baghdadi ne an kashe shi a wani harin hadin gwiwa da Amurka ta kai kusa da garin Jarablus na Syria.

Tarihin Abu Bakr al-Baghdadi

Abu Bakr al-Baghdadi, Shugaban Kungiyar IS da ke ikirarin jihadi kuma wanda ake gani shi ne wanda aka fi nema ruwa a jallo a duniya, ya kashe kansa ne yayin wani samame da sojojin Amurka suka kai a Arewa maso Yammacin Syria.

Kafin haka al-Baghdadi wanda ake yi wa lakabi da ‘Halifa Ibrahim,’ an sa Dala miliyan 25 a matsayin lada ga duk wanda ya kawo shi.

An shafe kusan shekara biyar Amurka da kawayenta na kokarin kama shi bayan da Kungiyar IS ta yi karfi a shekarar 2014.

An yi kiyasin cewa Kungiyar IS na da iko da kusan murabba’in kilomita dubu 88 daga yammacin Syria zuwa gabashin Iraki, kuma tana mulkin kama-karya ga kusan mutum miliyan takwas kuma ta samu biliyoyin daloli a matsayin kudaden shiga daga danyen man fetur, sata da garkuwa da mutane.

‘Wanda ya yarda da Allah’

Baghdadi – wanda sunansa na ainihi shi ne Ibrahim Awwad Ibrahim al-Badri – an haife shi a 1971 a garin Samarra da ke tsakiyar Iraki. A lokacin yana matashi, ana masa lakabi da ‘Wanda ya yarda da Allah,’ sakamakon tsawon lokacin da yake dauka yana zaune a masallaci yana karatun Alkur’ani kuma yana yawan caccakar wadanda ba su koyi da shari’ar Musulunci.

Bayan harin da Amurka ta kai da ya kai ga tarwatsa gwamnatin Saddam Hussein a 2003, an ce Baghadadi ya taimaka wajen samar da wata kungiyar jihadi mai suna ‘Jama’at Jaysh Ahl al-Sunnah wa-l-Jama’ah’ wadda ta rika kai hari ga sojojin Amurka da kawayenta.

A farkon 2004, sojojin Amurka sun taba kama Baghdadi a garin Falluja da ke yammacin Bagadaza inda suka tsare shi na kusan wata 10 a sansanin tsare masu laifi da ake kira ‘Bucca’ a Iraki. An bayyana sansanin Bucca a matsayin wata ‘jami’a’ ta manyan gobe amma ta Kungiyar IS, wanda wuri ne da wadanda aka tsare suka gauraya da sauran mutane suka san junansu kuma suka kulla kawance.

An bayyana cewa a lokacin da yake tsare a sansanin, ya yi limanci ya gudanar da hudubobi kuma ya koyar da darussa na addini kuma wani lokaci idan an samu rikici tsakanin wadanda suke tsare, jami’an da ke gudanar da sansanin kan sa al-Baghadadi domin ya shiga tsakani domin gudanar da sulhu.

A lokacin Amurka ta dauki al-Baghadadi a matsayin mutum wanda bai da barazana ga harkokin tsaro wanda wannan dalili ne ya sa aka sake shi bayan wata 10. Daya daga cikin jami’an ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya shaida wa jaridar New York Times a 2014 cewa ‘Dan dabar kan titi ne a lokacin da muka kama shi a 2004.’

Bayan ya bar sansanin Bucca, an yi zargin cewa al-Baghdadi ya samu haduwa da sabuwar Kungiyar Alka’ida da aka kafa a wancan lokaci. A lokacin, Abu Musab al-Zarkawi dan kasar Jordan shi ne ke jagorantar kungiyar.

A farkon 2006, Kungiyar Alka’ida ta Iraki ta kafa wata gidauniya mai suna ‘Mujahideen Shura Council’ wadda gidauniya ce da kungiyar da al-Baghdadi yake a wancan lokaci suka yi mata mubaya’a. A cikin wannan shekara ta 2006 bayan mutuwar Zarkawi sakamakon wani hari ta sama da Amurka ta kai, kungiyar ta sauya sunanta zuwa ‘Islamic State of Irak’ (ISI). Baghadadi a wancan lokacin shi ne ya ci gaba da sa ido a kwamitin shari’a na kungiyar kuma ya shiga Majalisar Shura.

A lokacin da aka kashe Shugaban ISI wato Abu Umar al-Baghdadi da Mataimakinsa Abu Ayyub al-Masri a wani hari da Amurka ta kai a 2010, an bayyana Abu Bakr al-Baghdadi a matsayin wanda ya gaje shi.

Karya Kungiyar IS

Cikin kusan shekara biyar da kungiyar ta shafe tana kai hare-hare a hankali, an yi kokarin fatattakar kungiyar daga wuraren da take da iko da su. Wannan yakin ya jawo asarar dubban mutane a kasashen biyu, ya kuma raba miliyoyin mutane da muhallansu, wuraren da ya shafa kuma wasu sun zama kufai.

A Iraki, sojojin kasar da mayakan Kurdawa sun samu goyon bayan Amurka da kawayenta da kuma jami’an tsaro masu kayan sarki na Iran. A Syria, sojojin hadin gwiwa na Amurka sun goyi bayan hadin gwiwar mayakan Kurdawa da mayakan Larabawa da kuma wadansu ’yan awaren Syria.

Jami’an da ke yi wa Shugaba Assad biyayya sun yaki IS tare da taimakon sojojin saman Rasha da wasu dakarun Iran. A yakin da aka shafe kusan shekara biyar ana gwabzawa, tambayar da ake yi ta ko al-Baghdadi na da rai ko ya mutu ta saka mutane cikin dimuwa.

An ciro rahoton daga Muryar Amurka da BBC