Search
Subscribe
Bayan Sallah za mu yi aure – Saurayin Baturiya

Isa Suleiman da wadda zai aura Janine Sanchez

Bayan Sallah za mu yi aure – Saurayin Baturiya

Saurayin nan da budurwarsa ‘yar Amurka ta biyo shi Kano mai suna Isa Suleiman Panshekara ya ce a bayan Karamar Sallah zai angwance da amaryarsa  Janine Sanchez.

Saurayin mai shekara 26 ya ce sun dage shagulgulan bikin nasu ne saboda wasu dalilai ba kamar yadda ake rade-radi ba a shafukan sada zumunta cewa saboda Shugaba Trump ya hana ’yan Najeriya shiga Amurka ne.

“Ka san komai yana iya canjawa, mun dage bikinmu zuwa mako biyu ko uku bayan Ramadan,” Isa Suleiman Panshekara ya shaida wa BBC.

Kazalika saurayin ya musanta cewa annobar cutar Coronabirus wadda ta karade sassan duniya ce, silar dage bikin.

Ganin cewa masoyiyar tasa mai shekara sama da 40 ta zo ta gan shi har gida kuma ta tafi, ko alaka tana nan yadda take a tsakaninsu? Sai Isa Suleiman ya ce:

“Sosai kuwa, yanzun nan kafin ka kira ni muka gama waya ta bidiyo, ka ga kuwa alama ce da ke nuna muna tare ba kamar yadda kafafen watsa labarai ke fada ba.”

Ya ci gaba da cewa: “Babu wani bambanci gaskiya, illa in ce ma so ne ya sake karuwa.

“Mafi yawa ta Facebook Messenger muke magana kuma waya muka fi yi ba rubutu ba (chatting) ba kamar Instagram ba inda muka fara haduwa.”

Isa Suleiman Panshekara ya ce ’yan uwa da abokan arziki na ci gaba da yi musu addu’a.

“Amma ka san ba za a rasa makiya ba, makiya kuma sai dai su je su yi ta yi,” inji shi.

Tun a watan Janairun bana ne labarin Isa da masoyiyarsa Ba’amurkiya ya baza shafukan sada zumunta, inda wadansu da dama ke tsokaci game da masoyan biyu masu bambancin shekaru.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin