✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan shekara shida, ana rubuta jarabawar WAEC a Chibok

A 2014 mayakan Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai sama da 200

Bayan shekaru shida, a bana Hukumar Shirya Jarrabawa ta Yammacin Afirka (WAEC) ta gudanar da jarabawa a garin Chibok na Jihar Borno bayan da hare-haren ‘yan Boko Haram ya hana yin haka a shekarun baya.

Mukaddashin Babban Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta ta bakwai, Birgediya Abdul-Khalifa Ibrahim ya bayyana hakan yayin wani taron kara wa juna sani da wata kungiyar mai suna EiEWGN ta shirya a Maiduguri ranar Alhamis.

A shekarar 2014 ne ‘yan Boko Haram suka sace ‘yan mata dalibai sama da 200 lokacin da suke jarrabawa a makarantarsu da ke garin na Chibok.

Yayin da aka sami nasarar ceto wasu daga cikinsu, wasu da dama har yanzu suna hannun ‘yan ta’addan.

Birgediya Abdul-Khalifa wanda kuma shi ne Kwamandan Shiyya ta Daya ta Rundunar Operation Lafiya Dole ya samu wakilcin Shugaban Ma’aikata na rundunar, Birgediya Ifeanyi Otu.

A cewarsa, “Dukkanmu shaida ne kan abubuwan da suka faru na sace ‘yan mata a Chibok, yanka wasu a Buni Yadi da kuma sace wasu Dapchi.

“Cikin ikon Allah yanzu wadannan duk sun zama tarihi sakamakon jajircewarmu.

“Abin farin ciki ne kasancewar bayan shekaru shida a bana dalibai sun samu damar rubuta jarrabawar WAEC bayan da sojoji suka samar da cikakken tsaro a makarantun”, inji Abdul-Khalifa.

Ya kara da cewa Rundunar Sojojin Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen farfado da harkar ilimi a yankin Arewa maso gabas ta hanyar bayar da cikakken tsaro.

Ya ce bayan da dakarunsu suka kwato garin Gwoza daga hannun ‘yan ta’addan sai suka yi amfani da malamai da suke cikin ‘yan gudun hijira wajen koyar da yara, suka kuma rika biyan su daga aljihunsu.

Ya ci gaba da cewa ko a kwanakin nan sai da suka bayar da tallafin littattafai ga sansanin ‘yan gudun hijira a jihar ta Borno.

Rundunar ta kuma ce tuni sojoji ta mika kaso 70 cikin 100 na makarantun da suke zama a ciki a da sakamakon kalubalen tsaro ga al’umma tare da cewa nan ba da jimawa ba ragowar kaso 30 din su ma za su bi sahu.