Da Dumi Dumi

Bayan shekara uku:  Ese ta kammala sakandare, Yunusa Yellow na can tsare a kurkukun Bayelsa

Shekara uku bayan an zargi Yunusa Dahiru da sacewa tare da yin garkuwa da Ese Oruru daga Jihar Bayelsa, inda ya kai ta Jihar Kano har aka bayar da rahoton daura musu aure, yanzu Ese Rita Oruru ta kammala makarantar sakandare, a daidai lokacin da ’yar da ta haifa ta cika shekara uku, yayin da Yunusa kuma ke can kurkuku a tsare. kamar yadda binciken Aminiya ya gano.

An zargi saurayin dan Jihar Kano, Yunusa Dahiru, wanda aka fi sani da Yellow  da yin garkuwa da Ese Oruru; ya mayar da ita  garinsu a Jihar Kano, a lokacin da Ese Oruru ke ’yar sheakara 13.

Bayanai sun ce, bayan faruwar wannan matsalar sai iyayen Ese Oruru, wadanda ke hada-hadar kasuwanci a Jihar Bayelsa sun  koma  kauyensu a Jihar Delta, inda suke rayuwa a halin yanzu.

’Yar Mista Charles da Misis Rose Oruru, wadanda ’yan asalin kauyen Uwheru a Karamar Hukumar Ughelli a Jihar Delta ne, an yi zargin cewa an aurar da ita ne ga Yellow ba tare da sahalewar iyayenta ba, sa’annan ta dauki juna biyu daga bisani.

A lokacin da take Jihar Kano, Ese Oruru ta musulunta; inda aka rada mata suna A’isha. Amma bayan haka, ’yan sanda a Jihar Kano sun kubutar da ita, tana dauke da cikin wata biyar, cikin da aka yi zargin na Yunusa Yellow ne.

ADVERTISEMENT

An gurfanar da Yunusa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Yenagoa a watan Maris, 2016 kan tuhume-tuhume biyar da suka hada da sace mutum da safarar yara da yin lalata da ci-da-ceto ta hanyar tare da yin jima’i ba bisa shari’a ba.

Wata majiya mai kusanci da iyalan Ese Oruru ta tabbatar wa Aminiya cewa, Oruru ta haifi jaririya a karshen shekarar 2016.

Malam Xahiru Bala, mahaifin Yunusa Yellwo

Bayan sace ta, gwamnatocin jihohin Bayelsa da Delta sun yi alkawarin tallafa mata; sai dai bincike ya gano cewa gwamnatocin biyu sun ki cika alkawuran da suka dauka.

Gwamnatin Jihar Bayelsa a nata bangaren, ta yi alkawarin bai wa Ese Oruru tallafin karatu; don ta samu damar komawa makaranta. Sai dai majiyarmu ta ce gwamnatin ba ta cika alkawarin ba.

Kodayake an ce sakamakon dalilai na tsaro, iyalan Oruru ba su iya zama a wani muhallin da aka kama musu haya a garin Yenagoa ba. Majiyarmu, wadda ta bukaci mu sakaye sunanta ta ce: “Gwamnatin ta kuma yi alkawarin samar wa mahaifiyar Ese jarin kasuwanci amma shiru kake ji. ’Yar da Esen ta haifa yanzu ta tasar wa shekara uku a duniya ta kuma kai munzalin shiga makaranta amma sakamakon wasu matsaloli ba za ta iya fara zuwa makaranta ba. Gwamnatin Jihar Bayelsa ta yi mana alkawarin bayar da tallafin karatu amma har yanzu ba mu sake ji daga hukumar bayar da tallafin karatun ba. Mun yi hijira zuwa Jihar Delta kuma daga nan karshen zancen ke nan.”

“Ko ita ma Gwamnatin Jihar Delta da ta daukar mana alkawari tun da farko; bayan komawarmu can, sai ta ce mana ai babu wani tanadi da ta yi mana. Don haka muke fatan Mai duka Ya albarkaci dan abin da ke gare mu wajen kula da ’ya’yanmu.”

“Ita Ese ta samu damar komawa makaranta; har ta kammala karatunta na sakandare. Da a ce gwamnatocin biyu sun cika alkawuransu, to kuwa da yanzu mun tsara yadda Ese Oruru za ta ci gaba da karatun gaba da sakandare. Sun tsame hannuwansu kwata-kwata daga gare mu, muna fama da matsalolinmu da kanmu,” kamar yadda majiyar ta tabbatar.

Aminiya har wa yau ta gano cewa Dahiru Yellow, wanda tun da farko Babbar Kotun Tarayya a Yenagoa ta bayar da belinsa a 2016, yanzu an kama shi tare da garkame shi a gidan yari, sakamakon keta sharuddan belin da aka ba shi.

A halin yanzu yana zaman jiran shari’a a kurkukun Yenagoa. Lokacin da wakilin Aminiya ya kai ziyara sashen shigar da korafe-korafe na Babbar Kotun Tarayya, wani jami’in kotun ya ki ya ce uffan a kan batun; sai dai ya bukaci wakilinmu ya nemi karin bayani daga hedkwatar hukumar gidajen yarin a Jihar Bayelsa.

Wakilin Aminiya a Kano ya gano cewa bayan faruwar lamarin, Yunusa Yellow ya koma gida Kano, inda ya yi ta gudanar da harkokinsa na kasuwanci, yana kuma kai-kawo tsakanin jihohin Kano da Bayelsa, domin halartar zaman kotun. Mahaifinsa ya  ce Yunusa ya kasance ba ya fashin halartar zaman shari’ar tasa amma sai a watan Mayun bana ya yi fama da jinya, wanda hakan ya sanya bai iya halartar zaman kotun ba har sau hudu. Bai sanar da kotun a rubuce ko kuma ta hanyar aika wakilinsa cewa bai da lafiya ba.

Kamar dai yadda bayanai suka tabbatar, rashin yi wa kotun bayani da Yelloiw ya yi, shi ya harzuka alkalin kotun wanda ya bayar da umarnin a ajiye shi a kurkuku don jiran shari’a; inda ya shafe wata uku a can.

Da yake magana da Aminiya, mahaifin Yunusa Yellow, Malam Dahiru Bala ya nuna damuwarsa game da halin da dansa ke ciki, yana mai cewa ba ya da wanda zai kula da al’amarinsa a can.

Ya ce, “Tun lokacin da ya bar kauyensa (Tungar-Danga) wata rana a watan Mayun bana, da zimmar zai je ya halarci zaman kotun daga bisani ya komo Kano, ba mu sake jin duriyarsa ba. Sai kawai ya kira ni a waya ya shaida mini cewa kotun ta bayar da umArnin a tsare shi a gidan kurkuku sakamakon kasa halartar zaman shari’ar tasa, har sau hudu.”

“Damuwata a nan, ita ce yadda nake fama da kula da karamar yarinyar da ya bari tare da matarsa a nan gida. Na kashe dan abin hannuna wajen kula da iyalinsa. Ban taba zuwa Bayelsa ba; don haka abu ne mai wuya a wurina in iya ziyartarsa. A gaskiya ni ban ma san yaya zan yi ko kuma ina zan je domin ganin dana ya dawo gida ba,” inji mahaifin.

Mahaifin ya kara da cewa yana magana ne da dan nasa ta hanyar jami’an gidan yarin; wadanda suke kiransa ta waya duk lokacin da dan nasa yake da bukatar su yi magana.

Ya ci gaba da cewa: “Na ziyarci Hukumar Shari’a ta Jihar Kano da kuma Hisbah, wadanda tun farko su ne suka dauki maganar kula da batun, sai dai babu wani abin kirki da na samu daga gare su. Damuwata a yanzu ita ce, yaya zan samu wanda zai dafa mini a wannan shari’a domin dawo da dana gida?”

Don haka sai ya bukaci Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Rano, Dokta Tafida Abubakar Ila da Kungiyar Lauyoyi Musulmi ta Najeriya (MULAN) da Hukumar Shari’a ta Jihar Kano da Hukumar Hisbah su yi maza wajen kawo masa dauki, domin dansa ya samu ya fita daga gidan yarin.

Ko da Aminiya ta tuntube ta, Huwaila Muhammad Ibrahim, wadda mamba ce a Kungiyar MULAN, wadda kuma tun farko ta shige gaba wajen samun belin Yunusa, ta ce ita a yanzu ta fita daga batun baki daya.

Huwaila ta ce, “Iya abin da na sani a nan shi ne, shi Yunusa ya keta belin da aka ba shi; sa’annan ya kasa halartar zaman kotun har sau hudu. Don haka alkalin kotun ya tsare shi a gidan yari don jirar shari’a. In fada maka gaskiya, ni dai a yanzu na tsame hannuna a cikin shari’ar. Ba ni da wata dangantaka da batun kwata-kwata. Duk abin da na yi a baya, na yi ne fisabilillahi. Amma a yanzu na fita daga batun.”

Shi ma dai Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Gidajen Yari a Jihar Bayelsa, Mista Eteiye Police, kawai alkawarin zai sake tuntubar wakilinmu ya yi, kuma bai tuntuba ba.

Share