Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Bayan ta ki shi shekara 50 baya: Fasto ya auri budurwarsa ’yar shekara 63

Ango da amarya Matthew Owojaiye da Abosede Igunnu bayan kammala daurin aurensu a Zariya
Ango da amarya Matthew Owojaiye da Abosede Igunnu bayan kammala daurin aurensu a Zariya

Masu iya magana sun ce matar mutum kabarinsa. Haka lamarin ya kasance a tsakanin wani Fasto da wata mata da ya nema da aure shekara 5o da suka gabata amma ta ki. Sai dai kuma a ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata Faston mai suna Matthew Owojaiye mai shekara 73 ya angwance da budurwarsa tasa mai suna  Farfesa Abosede Igunnu wadda ba taba aure ba duk da cewa yanzu tana da shekara 63 a duniya.                                                                                Cocin Living Faith  Church da ke Dogarawa a Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna ya cika ta batse da jama’a, wadanda suka taru don shaida bikin auren Fasto Owojaiye mai shekara 73 wanda ya auri wannan budurwa mai shekara 63 da mai suna Farfesa Abosede Igunnu, wadda ma’aikaciya ce a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Zariya.

Da yake yi wa Aminiya bayani kan yadda auren ya gudana, Fasto Joseph Yadunga na Majami’ar Libing Faith Church da ke Dogarawa, ya ce shi angon Owojaiye ya taba neman Abosede Igunnu don su yi aure kimanin shekara 50 da suka gabata, lokacin tana ’yar shekara 13 a duniya. Sai dai a wancan lokaci ta ce ita makaranta za ta yi, don haka sai ya hakura. Daga bisani dai shi ya yi aurensa har ya haifi ’ya’ya.

ADVERTISEMENT

Nemi Jaridar AMINIYA don karanta cikakken rahoton.

ADVERTISEMENT