✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan tube Sarki Sanusi II

An yi ta cacar baka a kafofin watsa labaran kasar nan da na kasashen waje, bayan tube Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Gwamnatin Jihar…

An yi ta cacar baka a kafofin watsa labaran kasar nan da na kasashen waje, bayan tube Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Gwamnatin Jihar Kano ta yi a ranar Litinin 9 ga watan  nan, bisa abin da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji ya kira rashin biyayya ga umarnin gwamnati da kin halartar tarurrukan alheri na gwamnatin jihar. Tube shi ke da wuya, sai aka wuce da shi zuwa garin Loko a Jihar Nasarawa, inda ya kwana daya. Bisa ga yawaitar koke-koken lauyoyinsa (Sarkin) da na kungiyoyin kare hakkin dan Adam, kashegari Talata Gwamnatin Nasarawa ta mayar da shi zuwa garin Awe, inda bayan share kwana uku a Awe, sai kuma aka dauki tsohon Sarkin zuwa Abuja a ranar Juma’a, bayan wata Babbar Kotun Tarayya ta ce a sakar wa tsohon Sarki mara ya sarara, don haka a ranar Asabar da safe ya samu isa Ikko, birnin Jihar Legas, Ikkon da aka ce tun farko can tsohon Sarkin na Kano ya zaba zai koma don zaman gudun hijirarsa.

Daya-da-daya, kamar yadda wadansu jama’a suke cewa, a ’yan shekarun nan, ba a yi wani Sarki a Arewacin kasar nan da Allah Ya yi wa baiwa da ilimin addinin Musulunci da na zamani da kudi da hazaka da nazari a kan al’amuran yau da kullum, musamman a kan fannin harkokin tattalin arziki da kuma bayyana ra’ayinsa kusan a kan kowace irin mas’ala musamman wadda ta shafi kasar nan, irin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ba, ba tare da la’akari da rawanin sarautar da ke kansa ba.

Wannan baiwa da Allah Ya yi wa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II, ita ta ba shi damar yake ji da iya magana a cikin wasu manyan harsunan duniya irin su Faransanci da Larabci, baya ga harshen Nasara wato Turanci. Masu irin wancan nazari sun ce sai dai kuma daga dukkan alamu tsohon Sarkin ya kasa zama lafiya da baiwar ilimin da Allah Ya yi masa.

Alal misali inji irin wadancan mutane, rashin iya zama da karatun nasa ya janyo a shekarar 2014, tsohon Sarkin a zamansa na Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya yi zargin cewa Kamfanin Man fetur na Kasa (NNPC), ya yi kwangen kudin man fetur da ya sayar da suka kai har Dalar Amurka biliyan 200 da bai zuba a cikin asusun ajiyar kudaden kasar nan ba. A takaice wannan furuci inji irin wadancan mutane, shi ya janyo Shugaban Kasa na wancan lokaci Dokta Goodluck Jonathan da rana kata ya bada shelar sauke Muhammadu Sanusi II, daga kan mukanminsa na Gwamnan Babban Bankin.

Allah cikin ikonSa yana zaman jimamin an cire shi daga kan mukamin Gwamnan Babban Bankin, a farko-farkon watan Yunin 2014, Allah Ya karbi ran Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, Sarkin Kano na 13 a Daular Fulani, sai Allah Ya ba Alhaji Sanusi Lamido Sanusi sarautar Kano. Saboda sanin hali, tun a wancan lokaci jama’a suka zuba idanu suka kuma kasa kunnuwansu, wajen ganin yadda Sarki Sanusi II, zai iya zura kafafunsa a cikin takalman wanda ya gada, Sarkin da ya san mulki, kuma ya iya mulki, Sarkin da Allah Ya ara wa lokaci ya share kusan shekara 51 a kan karagar mulki, Sarkin da ba kasafai kake jin muryarsa ba koda kuwa a cikin takwarorinsa sarakuna, sannan uwa uba Sarki Ado na da tsananin hakuri da na tare da shi da ma masu mulkin siyasa da  sauran talakawa.

Masu iya magana kan ce Sarki goma zamani goma, koda a kan zamani akwai gagarumin bambanci tsakanin lokacin mulkin Sarki Ado da na sarki Muhammadu Sanusi II, a kan girmamawa da ganin mutuncin sarauta da sarakuna da masu mulkin siyasa da talakawan wannan zamanin suke wa su sarakunan. Amma kuma a koyaushe kuma a ko’ina samun hakan ya dogara ne kan yadda su sarakunan suka iya taka-tsantsan da iya bakunansu tsakaninsu da masu mulkin siyasa da ma talakawansu. Ba ma tsakanin masu mulkin gargajiya da na siyasa ba, a koyaushe mutum shi ke ja wa kansa mutunci ko rashin mutunci a cikin rayuwar da ake. Muddin ka ja girmanka, ka kuma zama mai girmama na gaba da kai, to kuwa ba wanda zai taka ka.

Kamar yadda muka taso muka gani ko muka ji a lokacin mulkin Turawan mulkin mallaka har zuwa rushewar Jamhuriya ta Daya sarakuna (musamman a nan jihohin Arewa), su ke da wuka da nama dungurungum cikin tafiyar da mulkin talakawa, kama daga yin shari’a zuwa yanke hukunci, a karkashin ikonsu gidajen kurkuku da ’yan doka da yin tasarrafi da kudaden baitulmali da sauran ayyukan tsaron doka da oda, duk a hannun sarakuna suke. Sannu a hankali, canje-canje da garambawul na mulki da aka ratso tsawon lokaci suka sanya aka raba sarakunan gargajiyar da dukkan wadancan manyan ayyuka.

Abin da ya kai ya kawo, yanzu maganar da ake ba shadara daya  a duk dimbin tanade-tanaden da kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada ga sarakunan gargajiyar a zaman rawar da za su iya takawa cikin tafiyar da mulkin kasar nan da ya wuce bada shawara, walau ga Gwamnan jiharsu ko ga Shugaban Kasa. Kowa kuma ya sanya abin da ake nufi da bada shawara.

Da wannan ke nan mai karatu, duk wani basarake da ke son ya zauna lafiya da Gwamnansa lallai, shi zai nemi zaman lafiyar duk kuwa da kasancewar sarautar gargajiya wa’adinta na sai mutuwa ce ko kuma kaddara irin wadda ta samu Sarki Sanusi II, ta faru, alhali wa’adin mai mulkin siyasa kayyadajje ne. Da wannan nake ganin ashe duk Sarkin da yake so ya zauna lafiya da Gwamnansa, to kuwa ya zama wajibi ya kara jan amawalinsa ya rika yin gum da bakinsa.

Ina ma amfani ga Sarki ko sarakunan da ke, ko suke da ikon ganin  Gwamnan jiharsa ko Shugaban Kasa daya-da-daya kuma ido-da-ido, a kan bukatar talakawansu, amma kuma a ji shi, ko a ji su sana bada shawara ko suka komai ma’anarta ga Gwamnansa ko Shugaban Kasa a kan titi, koda kuwa wace irin gamsuwa ya sa ko suka samu a kowane hali.

Maganar sarauta ga Sarki Muhammadu Sanusi II (murabus), yanzu dai ta zama tarihi, kamar yadda shi ma ya fadi. Saura da me Allah Ya yi masa zabi mafifici, Ya kuma sa kaffara gare shi. Ga sauran sarakuna Allah Ya sa haka ya zame musu wata izina a kan yadda za su zauna da gwamnonin jihohinsu, wajen su kara jan amawalinsu. Da fatar dukkan wadanda su jagwalgwala waccan rigima tsakanin tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II da Gwamna Abdullahi Ganduje, yanzu za su saurara.