Da Dumi Dumi

Bayan wata 4 da tsare Zainab a Saudiya ta dawo Najeriya

Zainab Aliyu ta dawo gida Najeriya  bayan ta shafe fiye da watanni hudu a tsare a wajen hukumomi kasar Saudiyya.

Zainab ta dawo Najeriya ne a safiyar yau Litinin 13 ga watan Mayu da misalin karfe 10:00 na safe inda ta sauka a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA) da ke birnin Kano.

A watan Disambar 2018 ne dai jami’an tsaro a kasar Saudiyya suka kama Zainab Aliyu jim kadan bayan isarsu kasar domin yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma ‘yar uwarta Hajara. Jami’an tsaron sun zarge ta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.

Share