✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bazawara ta kashe kanta saboda an yi mata fada

Wata bazawara mai shekara 26, mai suna Fatima Jibrin da aka fi sani da Talatuwa da ke zaune a garin Lere da Karamar Hukumar Lere…

Wata bazawara mai shekara 26, mai suna Fatima Jibrin da aka fi sani da Talatuwa da ke zaune a garin Lere da Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna, ta kashe kanta saboda yayanta ya yi mata fada kan zagin mahaifiyarta da take yi.

Da yake yi wa wakilinmu bayanin yadda al’amarin ya faru, wani yayan marigayiyar mai suna Lawal Aliyu Lere ya ce marigayiyar ta kasance mara jin magana, kuma duk abin da ’yan uwanta suke yi suna kokari ne su jawo hankalinta ta zama tagari.

“Abin da ya faru har ya kai ga wannan al’amari ana yi mata fada ne kan ta bi  mahaifiyarta domin mahaifiyarta ba a  bar wulakantawa  ba ce. Shi ne wani yayanmu ya ce duk ranar da ya ji ta sake cin mutuncin mahaifiyarta,  zai yi mata duka.”

Ya ce da ta fita daga gida ba a sani ba,  sai ta je ta sayi fiya-fiya a wani shago da ke kusa da gidansu ta sha. Bayan ta dade da shan wannan guba ce, sai take fada wa mutane cewa ta sha fiya-fiya, kafin a kawo mata dauki sai ta rasu.

Ya ce bayan faruwar wannan al’amari, babu wani mataki da suka dauka saboda ita ce da kanta ta yi wannan abu. Don haka aka shirya aka yi mata jana’iza, aka yi mata addu’o’in Allah Ya gabafarta mata.

Ya ce marigayiyar ta yi aure har ta haifi ’ya’ya biyu amma auren ya mutu shekara biyu da suka gabata, don haka take zaune a gida.

Wakilinmu ya tuntubi Magajin Garin Lere Alhaji Yakubu Sulaiman Lere kan wannan al’amari, domin jin ta bakinsa inda ya ce gaskiya ba su ji dadin faruwar wannan al’amari ba, inda ya ce ba a taba samun irin wannan al’amari ba a garin.

Ya yi kira ga matasa maza da mata su rika bin maganar iyayensu, domin su rabu da iyayensu lafiya kuma su gama da duniya lafiya.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo kan wannan al’amari ta waya, amma bai same shi ba.