✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

BCO ta bukaci EFCC ta binciki tsohon shugaban TETFund

Kungiyar yakin Neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wato ‘Buhari Campaign Organization’ (BCO) ta yi kira ga Hukumomin EFCC da DSS da su binciki tsohon…

Kungiyar yakin Neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wato ‘Buhari Campaign Organization’ (BCO) ta yi kira ga Hukumomin EFCC da DSS da su binciki tsohon Shugaban Hukumar TETFund, Dakta A.B Baffa.

Kungiyar ta BCO ta yi wannan kira ne a yau a wata takardar manema labarai da Daraktan Sadarwa da tsare-tsare, Malam Ibrahim Gidado ya sanya wa hannu.

Kungiyar BCO ta shelanta cewa, akwai matukar bukatar hukumar EFCC ta kama tsohon Sakataren, A.B Baffa ne saboda abubuwan da ta kira ta’asa da ya aikata yayin da a ka ba shi amanar hukumar TETFund, inda ya yi amfani da wannan damar wurin cin amanar kasa a hukumar ba bisa ka’ida ba.

Haka kuma takardar ta BCO ta bayyana cewa; “A kokarin zabo nagartattun mutane wadanda a ka yi musu shaidar gaskiya da rikon amana ne ya sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Ministan Ilimi suka dauko Dakta A.B Baffa domin ya ja ragamar Hukumar Ilimi ta TETFund. Musamman ma don a samu daidaito, cigaba da bunkasa harkokin ilimi.

“Kafin a dauko A.B Baffa sai da a ka yi la’akari da irin jajircewarsa a lokacin da yake shugabantar Kungiyar malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Bayero, Kano da kuma lokacin da ya jagoranci kungiyar ASUU din a matsayin shugaba na shiyya. Wannan ya sa a ka kyautatawa A.B Baffa zato da cewa, zai kawo ci gaban da gwamnatin Muhammadu Buhari ke fatan gani a fannin ilimi.

Haka kuma, Kungiyar ta BCO ta yi fashin baki kan wasu daga cikin dalilan da suka sa gwamnatin Muhammadu Buhari ta tsige Baffa a matsayin Sakataren Hukumar TETFund, inda ta bayyana cewa, ya wulakanta kujerarsa da ofishinsa ta hanyoyi da dama.

“Daga cikin dalilan tsige shi akwai batun dakile malamai masu karo karatu a kasashen ketare. Inda ya yi ta muzanta su, tare da yi musu hawan kawara. Ya yi amfani da ofishinsa wurin musgunawa da yawan malaman da ke karatu a wasu kasashe, ta hanyar ayyana makarantunsu a matsayin wadanda basu dace a yi karatu a cikinsu ba.

“Haka kuma ba da yawun Gwamnatin Shugaba Buhari ba ne A.B Baffa ya kutsa kanshi cikin siyasa. Wanda hakan na daga cikin dalilan da suka sa dole a bincike shi kan yadda ya tafiyar da dukiyar Hukumar ta TETFund. A kan wannan ne ma ya sa muke kira ga EFCC da ta kama shi domin yi mas tambayoyi.” Inji BCO

Kungiyar BCO ta ce; “Ya kamata Hukumar DSS ta kama A.B Baffa ne bisa irin kalaman tunzarawa, bata suna da ya yi ta faman yi. Domin ba zai yiwu don Shugaban Kasa ya tsige shi ya koma yana yin yarfe ga gwamnati, da kokarin tunzara al’umma. Duk kuwa da cewa, A.B Baffa ya kwana da sanin cewa, doka ta ba Shugaban qasa dama ya tsige shi ko da kuwa bai aikata laifin komi ba. Alhali shi kwance yake dumu-dumu cikin laifuka, take hakki, da almundahana, wanda malaman Jami’o’i sun fi kowa sanin haka.” a cewar Kungiyar ta BCO.