Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Bello Muhammed Bello zai yi kwal-kwabo domin cika alkawari

Fitaccen jarumin Kannywood, kuma Darakta Bello Muhammed Bello wanda aka fi sani da General BMB zai cika alkwarinsa na aske gashin kansa idan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake lashe zaben Shugaban Kasa.

BMB ya bayyana haka ne a shafinsa na Instagram, inda ya kara da cewa taron bikin saisayen zai wakana ne a Jihar Kaduna.

ADVERTISEMENT

Idan ba a manta ba, Aminiya ta rawaito BMB wanda darakta ne kuma mai tsara labaran fim kafin zabe yana cewa duk da cewa wani furodusa ya taba tayin ba shi Naira miliyan 1 da dubu 500 domin ya yi kwal-kwabo don ya fito a wani fim, amma ya ki saboda irin yadda yake son tara gashi a kansa wanda yake tara wa na tsawon shekara 10 da suka wuce ba tare da aske ba.

A lokacin da yake daukar alkawarin, BMB ya ce, “Idan har aka bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zabe, zan yi kwal-kwabo domin nuna yadda nake son Shugaba Buhari din. Na yi wannan alkawarin ne domin in kafa tarihi.”

ADVERTISEMENT

Da yake sanar da shirinsa na cika wannan alkawari da ya dauka a wani faifan bidiyo, BMB ya ce Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai zai halarci bikin, amma bai fadi ranar da za a yi bikin ba.

BMB wanda yana daya daga cikin jaruman Kannywood da suka dade ana yi da su yana cikin jaruman Kannywood da suka taya Shugaba Buhari yakin neman zabe.