✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Benteke zai shafe makonni shida yana jinya

Manajan kulob din Aston billa da ke Inigla Paul Lambert ya bayyana cewa dan kwallon gabansu, Christian Benteke, zai share mako shida yana jinya bayan…

 Christian BentekeManajan kulob din Aston billa da ke Inigla Paul Lambert ya bayyana cewa dan kwallon gabansu, Christian Benteke, zai share mako shida yana jinya bayan raunin da ya samu a wasan da kulob din ya yi da na Norwich City a gasar rukunin Premier ta Ingila a makon jiya.
Gwajin da likitocin kulob din suka yi wa dan kwallon ya tabbatar dan kwallon ya samu raunin da zai shafe makonni biyar zuwa shida ba tare da ya yi kwallo ba.
Manajan ya hori takwarorin Benteke musamman ’yan wasan gaba a kulob din da su zage damtse don ganin sun cigaba da samun nasara kafin dan kwallon nasu ya murmure.
Manajan ya ce hanya daya da za ta nuna takwarorinsa sun damu da halin da yake ciki ita ce su cigaba da samun nasara a wasanni masu zuwa.
Da wannan rauni da dan kwallon ya samu, ba zai samu buga wasanni da suka hada da na zumunta da kasarsa Beljiyam za ta yi a kwanaki masu zuwa ba.
Aston billa ta doke Norwich City ne da ci 1-0 a wasan.